1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar yaduwar murar tsuntsaye a Turai

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOp

Ministocin harkokin wajen kasashen KTT sun gudanar da wani taron gaggawa a Luxemburg, inda suka tattauna akan barazanar da ake fuskanta ta murar tsuntsaye. Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw, wanda kasarsa ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar EU ya fadawa manema labari cewa an dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen tinkarar kwayoyin cutar idan suka kasance ana iya kamuwa da su tsakanin ´yan Adam. Wannan taron dai ya zo ne a daidai lokacin da Girika ta ce tana binciken wabin da ta kira murar tsuntsaye ta farko da ta bulla a tsibirin Aegean. Yanzu dai jami´an kiwon lafiyar kasar na gudanar da gwaji don tabbatar da ko nau´in cutar mai hadarin ne wato H5N1 wanda aka gano a kasashen Romaniya da Turkiya.