1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar 'yunwa a Sahel

June 19, 2010

Anyi kira ga ƙasashen duniya, da su gaggauta kai ɗaukin cimaka a ƙasashen yakin Sahel.

https://p.dw.com/p/NxcZ
Wani yaro mai fama da yunwa a NijarHoto: AP

Ƙungiyoyin ba da agaji sun bayyana fargaba, bisa bala'in 'yunwa da ake fama da shi a yankin Sahel. Ƙungiyar "Save the Childeren" ta ce, duk da cewa ƙasashen duniya sun yi alƙawarin ba da taimkon cimaka ga ƙasashen Nijar da Chadi, amma har yanzu ba'a taɓuka wani abun azo agani ba. Manajan ƙungiyar a yankin yammacin Afirka, Malik Allaouna yace wannan lamarin yana iya zama wani babban bala'i nan da 'yan kwanaki masu zuwa, inda ƙungiyar ta ce yanzu haka 'yunwa ta fara barazana ga rayuwar dubban yara a ƙasar Nijar. Jami'in ya ce abin da suke faɗi shine, yanzu haka anyi jinkiri ƙwarai. Ƙungiyar "Save the Children" ta ce ganin ana cikin lokaci na bazara, abin da ake da shi a rubbu ya ƙare kana ana jiran sabon kaka. Rohotonni suka ce rashin isasshen damana a bara, daga ƙasar Mauritaniya izuwa Sudan, zai haddasa masifar yunwa fiye da wanda aka gani a shekara ta 2005.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas