1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BARNAR DA CUTAR AIDS KEYI A NAHIYAR AFRICA DA KUMA DUNIYA:

January 8, 2004
https://p.dw.com/p/Bvmi
Hausawa dai kance shekara kwana,yau kwanaki bakwai ke nan da wucewar shekara ta 2003.
Rahotanni daga nahiyar Africa sun tabbatar da cewa,cutar da tafi addabar mutanen kasashen kudu da hamadar sahara a shekara data gabata itace ta kanjamau,ko kuma sida a turance kuma Aids.
Da yake yanzu an shigo sabuwar shekara,bayanai sun shaidar da cewa wadan nan kasashe da wannan cuta tafi yiwa taadi,nayin shakulatin bangaro wajen ci gaba da daukar matakan kawar da ita baki daya.
An dai kiyasta cewa kusan mutane miliyan 42 dake dauke da wannan cutar a duniya,miliyan 30 daga cikin su sun fito daga wannan nahiya ta Africa ne,kuma da dama daga cikin su matasa ne.
A kuwa ta bakin wata hukumar lafiya mai suna Pathfinder dake zaman kanta a birnin Nairobin kenya,cewa tayi muddin wadan nan kasashe na Afric a suka bar irin wannan lamari naci gaba yadda yake a yanzu dangane da cutar ta aids to babu shakka za,a samu matasa dake da shekaru daga 15 zuwa 24 da zasu rasa rayukan su daga nan zuwa shekara ta 2005.
A kuwa ta bakin wani jamiin kasar Amurka mai kula da bangaren yaki da cutar aids a duniya,MR Randal Tobias , cewa yayi,idan ba,ayi hankali ba, mutane da zasu kamu da wannan cuta ta aids daga nan zuwa shekara ta 2010 yawan su zai kai miliyan 85.
Za kuma ayi asarar rayukan mutane kusan miliyan 100 daga wannan shekara ta 2010 izuwa ta 2020.
MR Tobias yaci gaba da cewa, a shekara ta 2002 data wuce kawai kusan mutane miliyan uku ne suka rugamu gidan gaskiya saboda kamuwa da wannan cutar ta Aids,ban da kuma wadanda suke cikin halin galabaita na rashin inda zasu saka kansu saboda kamuwa da cutar.
Ita kuwa hukumar kula da asusun tallafawa kana nan yara ta fannin ilimi da kuma raya al,adu ta Mdd cewa tayi muddin aka bar cutar ta Aids taci gaba da yaduwa a nahiyar ta Africa kamar yadda take a yanzu haka to babu makawa,za,a bar yara ka na cikin halin kaka ni kayi na rashin iyaye.
A yanzu haka a cewar hukumar ta UNICEF, kasar da tafi kowace kasa yawan yara kana na marayu saboda kamuwa da iyayen su sukayi da wannan cuta ta Aids itace Nigeria, dake da yara marayu 995,000. Daga nan kuma sai,Habasha mai 989,00 sai Congo mai 927,00 sai Kenya mai 892,00 daga kenya kuma sai Uganda mai 884.
Daga Uganda sai Tanzania,mai 815,00 sai Zimbabwe mai 782,00 daga nan kuma sai Africa ta kudu mai 662,00 a karshe kuwa sai Zambia mai 557,00. Babban abin bakin ciki a cewa Tobias shine da dama daga cikin masu kamuwa da cutar ta Kanjamau da kuma masu mutuwa dukkannin su matasa ne wadanda keda jini a jika:
Bisa irin wannan halin da ake ciki kuwa,kasar Amurka ta bayar da sanarwar taimakon kudi dala billiyon 15 don kula da wadanda suka kamu da cutar Kanjamau miliyan biyu a Nahiyar Africa tare da taimakon yara marayu wadanda iyayen su suka mutu saboda kamuwa das cutar ta Kanjamau.
Haka itama kasar Japan ta taimaka da kudi har dala miliyan 15 ga kasashen Zimbabwe da swaziland don kare yaduwar wannan cuta ta Kanjamau a tsakanin matasan kasar.
A hannu daya kuma Mdd ta hanyar hukumominta har yanzu naci gaba da taimakawa wajen dakile yaduwar wannan cuta ta Kanjamau a nahiyar ta africa.