1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun Kaura daga ƙasa zuwa ƙasa

Zimmermann, Martina February 22, 2008

Ƙokarin kyautata rayuwar Baƙi 'yan ci rani a Turai

https://p.dw.com/p/DC1j
Bakin haure dake kokarin shiga Turai.Hoto: picture-alliance/dpa

A shakarun 1960 zuwa sama ƙaura daga wata kasa zuwa wata kasa ta kai kololuwarta, kuma kawo yanzu ma mutane masu kauracewa ƙasasshen su zuwa wasu ƙasashen duniya domin neman ayyuka da kyautata matsayin rayuwa, sai karuwa suke yi.

Domin kara kyautata matsayin 'yan gudun hijira, ƙungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziki ko kuma (OECD) ta shirya wani taro na ƙasa da ƙasa ranar laraba da ta gabata a birnin Paris, don kir-kiro sabbin hanyoyi da za'a iya ɗauka wajen kyautata jin- daɗin baƙi 'yan ci rani.

Duk da cewar mafi yawa daga cikin al'umar ƙasar Luxemburg baƙi 'yan ci rani ne, inda kusan kashi 32 daga cikin 100 suke haifaffun wasu ƙasashe, amma kuma Amirka ita ce kan gaba wajen yawan baƙi 'yan ci rani. Yanzu hakan Amirka na da baki fiye da miliyan 31. Kasar Jamus ita ce ta biyu a jerin ƙasashe masu yawan baki, sai ƙasashen Faransa, Canada da Britaniya.

Rahotanni sun nuna cewar ba shakka nan gaba kadan wasu kasasahe zasu bukaci baki wadanda zasu taimaka wajen gudanar da aikace aikace. Wani masana kan harkokin samarwa baki ayyukan yi, Thomas Liebig ya ce babu shakka wannan wani abu ne da ya kamata a mayar da hankali kansa:

"Mun fara mayar da hankali kan matakai na kara kyautata makomar baki 'yan gudub hijira. Kuma kamar yadda abubuwa ke tafiya a wasu 'yan kasashe kalilan, za'a bukaci baki wajen gudanar da wasu aikace aikace. Misali kasar Jamus na cikin kasashen da zasu fuskanci karancin ma'aikata nan da shekaru 5 zuwa 10 masu zuwa, kuma mai yiwuwa ta shiga neman ma'aikata daga kasashe daban daban na duniya domin samun koma baya wajen yawan ma'aikata. Amma idan haka ya faru, dole ne mu tabbatar da an zama na cudanya tsakannin al'uma da wadannan baƙi 'yan ci rani."

Da yawa daga cikin baƙin za'a tarar suna da ilimi dai dai kamar 'yan ƙasa, kusan daya daga cikin hudu na baki 'yan ci rani na da ilimi mai zurfi, a wani lokacin ma za'a a ga cewar wasu bakin ma suna da ilimi mai zurfi, fiye da 'yan kasar, inda za'a tarar kashi 19 cikinsu ne kawai ke da ilimi dai dai da na baƙin. Amma abin mamaki a nan shi ne, bakin na fuskantar matsala wajen samun ayyuka da suka dace da irin ilimin da suke dasu. Thomas Liebig ya kara da cewa, da yawa daga cikin wadannan baki suna ayyuka da su dace da yawan ilimin da suke da shi ba;

"Ko wace kasa na da irin salo da ta ke amfani da shi wajen rarraba ayyuka ga jama'a. Misali nan Jamus inda ake fuskantar matsalolin baki 'yan ci rani tare da baki da suka kwararo cikinta daga sauran kasashe makwabta, inda bayan fadada kasashen EU ta samu baki kusan miliyan 3 da digo 5 da suka shigo, babu wani mataki da kampanoni da ma'aikatan gwamnati ke dauka wajen bawa wadannan mutane ayyuka da suka dace da iliminsu. Nan kasar Kampanoni da ma'aikata masu zaman kansu sukan bawa bakin ayyuka da suka tabbatar sa su karu dasu, misali mutun mai zurfin ilimi zai iya samun aiki irin na wadanda basu ko yi makaranta ba, sabili da ma'aikata da kampanoni na daukan matakai da zasu ci riba dasu kawai."