1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batutuwa kan adadin 'yan gudun hijira a Jamus

Abdourahamane Hassane/ SBAugust 24, 2016

Bisa ga dukkan alamu akwai karancin bayannai kan adadin 'yan gudun hijira da ke shigowa kasar Jamus da ma kan kudaden da ake kashewa a kansu a cewar kwararru.

https://p.dw.com/p/1JoQt
Deutschland Flüchtlinge bei Wegscheid
'Yan gudun hijira da suka shigo cikin kasar JamusHoto: picture-alliance/dpa/S. Kahnert

Wani abin bakinciki kamar yadda ofishin tarraya da ke kula da 'yan gudun hijira na Jamus ya nunar, shi ne cewar addadin na 'yan gudun hijirar ba shi da sahihanci saboda yawancin wadanda aka yi rejistan na su da suka shigo kasar babu wasu bayanai da suka shafesu, irin su fasfo da wasu sauran takardun shaida. Don haka yana da wahala a san adadin 'yan gudun hijirar da ke shigowa a kasar. Abin da ke tabbas shi ne cewar a yanzu an soma samun karanci na 'yan gudun hijira da ke shigowa Jamus domin alkalluma sun nunar cewar a cikin watan Yuni na 2016 an samu shigar 'yan gudun hijira 16.300 yayin da a cikin watan Janeru na farkon shekarar aka samu 91.600.


Sai dai kuma adadin masu neman mafaka ya karu kamar yadda ofishin tarraya da ke kula da 'yan gudun hijirar watau BAMF ya nunar, wanda ya ce a shekarar bara an samu kusan masu neman mafaka 441,899 amma kuma a wannan shekarar aka samu kamar mutum 468.762 a karshen watan Yuli duk da ma cewar ana samu tafiyar hawainiya wajen bayar da mafakar. Christian Proano masanin tattalin arziki ne da ke a jami'ar Bamberg a nan Jamus:

Deutschland Integration Migranten in Ausbildungsberufen
Kula da samawar wa 'yan gudun hijira ayyukan yi a JamusHoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

''Dole ne mu yi gaggawar ganin a shigar da wadan nan masu neman mafaka a cikin harkokin rayuwar yau da kullum na Jamus don ganin sun samu kwarewar da ta dace da gaggawa, kuma a bar ganin kamar kudaden da za a kashe saboda wannan aiki a matsayin kamar asara, domin zai kasance jari ga tattalin arzikin Jamus a gaba.''

Kowa ne dan gudun hijira dai na bukatar ci da sha da samun illimi da aiki da kuma kula da kiwon lafiyarsa, sannan bincike da cibiyoyin nazararin tattalin arzikin na Jamus DIW da ke Berlin suka yi da kuma IFO da ke a birnin Munich da IW da ke a Kologne da cibiyar IFW ta duniya baki daya, da kuma cibiyar nazari ta nahiyar Turai baki daya watau ZEW da ke a Mannheim su dukkaninsu sun nuna cewar a kowacce shekara abin da za a iya kashewa dan gudun hijira ya tashi tsakanin Euro 12.000 zuwa 20.000.

A sakamakon wannan nazarin da cibiyoyin suka yi ofishin ministan kudi na Jamus ya ware kimanin biliyan 99,8 na EURO zuwa biliyan 20 a kowacce shekara domin kulawa da 'yan gudun hijirar tun daga shekara ta 2016 har zuwa 2020.

Deutschland Flüchtlinge bei Wegscheid
'Yadda ake tattance 'yan gudun hijira masu shigowa JamusHoto: picture-alliance/dpa/A. Weigel