1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayanai game da ƙasar Australiya

October 14, 2010

Taƙaitacen tarihi game da ƙasar Astraliya: Ina take, yawan jama´arta, da ƙasashen da ta yi iyaka da su.

https://p.dw.com/p/PePn
Ƙasar AustraliyaHoto: DW

Na farko mu sanar a takwara na cewar an karkasa duniya  a nahiyoyi guda biyar wato Afrika ,Turai, Amurika, Asiya da Oceaniya.Ita ƙasar Australiya ta na cikin Osheyaniya wanda gaba ɗanyanta ruwa teku ne kewaye da ita.

Idan mu ka ɗauka da Najeriya ,Australiya na kudu maso gabas.

Ruwa  ke kewaye da Australiya, amma idan ka ƙetara ruwan, a ɓangaren arewa ta yi iyaka da Indonesiya ,Timor ta gabas,da Papua sabuwar Guinea. A ɓangaren arewa maso gabas, ta yi iyaka da Tsibirin Salomon da Vanuatu, sai kuma ƙasar Nuzelan a kudu maso gabas.

Australiya na da yawan al´uma miliyan 22 wanda mafi yawan su ke zaune a cikin manyan biranen ƙasar kamar su Sydney inda aka yi wasan Olympic , Canbera wanda shine babban birnin ƙasar, Melbourne da dai sauran birane.

Mafi yawa daga al´umar Australiya krista ne mabiya ɗariƙar katolika, amma akwai kashi 1, 6 musulmi, sai kashi 16 wanda ba su da addini.

ƙasar Australiya ta samu ´yancin kanta daga turawan mulkin mallakar ƙasar Birtaniya ranar ɗaya ga watan Janairu na shekara 1901 wato shekaru 109 kenan daidai.

Ta fannin ƙarfin tattalin arziki, ta na sahun ƙasashe masu ci gaban masana´antu.A shekara 2008 alƙalluman Majalisar Ɗinkin Duniya, sun jera Autsraliya a matsayin ƙasa ta 14 ta fannin ƙarfin tattalin arziki a duniya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal