1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

241010 WikiLeaks USA Reax

October 25, 2010

Gwamnatin Amirka ta nuna rashin jin daɗinta game da bayanan sirrin aikin sojinta a Iraƙi da WikiLeaks ya wallafa

https://p.dw.com/p/PnmL
Shugaban Wikileaks Julian Assange (dama) a taron manema labaru na haɗin guiwa a LondonHoto: dpa

A ƙarshen mako ne shafin nan na Internet da ake kira WikiLeaks ya sake wallafa dubban bayanan sirri na sojojin Amirka kan yaƙin Iraƙi. Kuma ko da yake gwamnatin Amirka ta yi takatsantsa a martanin da ta mayar dangane da haka, to amma tambayar da ake yi ita ce yaya girman lahanin da hakan zai yiwa mutuncin ƙasar ta Amirka?

Masu iya magana kan ce wai shiru ma jawabi ne. Duk da cewa kafafen yaɗa labarun Amirka sun ba da rahaotanni da dama game da sabbin bayanan sirrin da shafin na Internet ɗin wato WikiLeaks ya wallafa, amma martanin da shugabannin siyasa suka mayar ba yawa. Muhimmin abu ga 'yan siyasar a yanzu shi ne zaɓen 'yan majalisar dokoki da zai gudana nan da mako guda, saboda haka sha'awar ba da muhammanci ga wani labari maras daɗi daga iraqi kaɗan ce. Hakazalika yaƙe-yaƙen da Amirka ke yi ba sa taka wata rawar a zo a gani a yaƙin neman zaɓen. Wato shugabannin siyasa a Washington sun yi shiru in ban da wani jawabi kan wannan batu da kakakin ma'aikatar tsaro Geoff Morell yayi, inda ya yi suka da kakkausan lafazi game da wallafa bayanan da WikiLeaks yayi, domin zai saka rayukan sojojin Amirka da na ƙawayenta da kuma na Iraqi cikin haɗari.

"Waɗannan gajajjerun rahotanni ne daga filin daga da aka ɗauka cikin gaggawa. Ba sa bayanin gaskiyar abubuwan dake faruwa a wannan rikici. Ba mu ga wani sabon abu a ciki ba game da abubuwan da suka faru a cikin shekaru tara da suka wuce."

Da yawa daga cikin kafofin yaɗa labarun Amirka ma na masu ra'ayin cewa rahotannin ba su ƙunshi wani sabon bayani mai gamsarwa ba. To amma sun yi nuni da muhimman abubuwa na wannan yaƙi. Alal misali dangane da yawan mutanen da yaƙin ya rutsa da su kawo yanzu. Alƙalumman da rahotannin suka bayar musamman na fararen hula da rikicin ya rutsa da su, sun fi waɗanda ma'aikatar tsaron Amirka ta bayar ya zuwa yanzu. Wato 'yan Iraƙi dubu 109 kuma biyu bisa uku fararen hula da suka rasu a cikin shekaru shida sakamakon rikicin.

Saɓanin takwarorinsu na Amirka, kafofin yaɗa labarun ƙasashen Larabawa sun ɗauki bayanan da WikiLeaks ya wallafa da muhimmanci, inda suka ce adadin mutanen suka mutu ko suka ji rauni ya kai dubu 285.

Tambayar da ake yi a Amirka yanzu ita ce girmar lahanin da bayanan suka yiwa mutuncin Amirka a Iraƙi. Musamman rahotannin da suka zargi sojojin Amirka da nuna halin ko oho ga azabtar da firsinoni da dakarun tsaron Iraƙi suka yi. Ga dai kakakin ma'aikatar tsaron Amirka Geoff Morrell.

"Muna magana ne game da wata ƙasa mai cikakken 'yanci wadda ke da rundunar sojinta kuma take da dokokin tafiyar da al'amuranta. Aikinmu shi ne mu miƙa irin waɗannan rahotanni na cin zarafin ga sashen da abin ya shafa a rundunar Iraƙi domin su ɗauki matakin da ya dace."

Shi ya sa zargin cin zarafin ya zama batu ne na Iraƙi kaɗai. Jaridar New York Times ta ce sam ba haka ba ne domin ai shugaba Barak Obama ya mayar da samar da dakarun tsaro a Iraƙi masu inganci a matsayin sharaɗin shirinsa na janye sojojin Amirka daga ƙasar.

A halin da ake ciki Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga cikin wannan muhauwara, inda mai kula da batun cin zarafi na majalisar yayi kira ga Obama da ya kafa kwamitin binciken wannan zargin.

Mawallafa: Sabine Müller / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas