1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayanin gwamnati a majalisar dokokin Jamus kan Afghanistan

April 22, 2010

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel tayi wa majalisar dokoki ta Bundestag bayani kan Afghanistan

https://p.dw.com/p/N35C
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a majalisaHoto: AP

Tun kafin shugabar gwamnati, Angela Merkel ta ta fara bayanin ta, sai da yan majalisar dokokin suka mika daga kujerun su, suka yi tsayuwar juyayi ga sojojin na Jamus bakwai da suka rasa rayukan su a Afghanistan tun dfaga lokacin easter.

Majalisar dokoki ta Bundestag da al'ummar Jamus mazan su da matan su, suna nuna girmamawar su ga wadanda suka mutu. Ga wadanda suka bari kuma, muna nna matukar matukar rashin jin dadi da ta'aziyyar mu. Sojojin mu dake fama da raunuka, muna masu fatan samun sauki cikin gaggawa.

Wadannan sune kalmomin kakakin majalisar dokokin Jamus, Nobert Lammert wanda ma ya tunatar da gagarumin alhakin dake kan majalisar dokokin ta Jamus, sakamakon tura sojojin da tayi zuwa Afghanistan. Ita ma shugaban gwamnati, Angela Merkel, tayi magana a game da shakkun dake zukatan jama'a a sakamakon mutuwar sojojin.

Tace wannan shakka kuwa, ta shafi ko tura sojojin na Jamus zuwa Afghamnistan abu ne da a zahiri ya zama wajibi, wanda babu yadda za'a iya kauce masa.. Sai idan mun kawar da wadnanan shakku ne zamu iya nunawa jama'a bukatar aikin sojojin zamu a can. Wannan akalla shine yadda nake gani. Amma duk da haka ni kaina, kamar mafi rinjayen wkailan wnanan majalisa, ina goyon bayan abin da sojojin namu suke yi.

Shugaban gwmnatin ta Jamus tace dalilin tura sojojin na Jamus a Afghanistan shine tsoron cewar kungiyar yan tarzoma ta al-Qaeda, tana iya sake shirya wasu hare-haren na ta'addanci daga Afghanistan. Saboda haka aikin da sojojin suke yi a Afghanistan shine su tabbatar da tsaron Jamus, saboda ita ma Jamus din bata fita daga idanun yan tarzoma a hare-haren su ba.. Duk kuwa wanda ya nemi janye sojojin na Jamus yanzu-yanzu, to kuwa ana iya cewa tunanin sa bai kai ko ina ba.

Angela Merkel tace izinin da majalisar dokoki ta Bundestag ta baiwa aiyukan na sojojin Jamus a Afghanistan, izini ne da yake kan doka, kuma bisa ka'ida. Wannan bayani ya zama daura da bukatar da shugaban jam'iyar adawa ta SPD Sigmar Gabriel ya baiyana, ta gabatar da sabuwarf doka amajalisar da zata shimfida sabon tsarin aiyukan da sjojin suke yi a Afghanistan. To ssai dai a majalisar dokokin, shugaban jam'iyar adawa da tafi girma, ya nuna cikakken goyon bayan sa ga dopkar dake aiki yanzu.

Yace muna nuna cewar muna sake da alhakin dake kanmu na kasa da kasa a game da aiyukan sojojin, amma tilas ne mu sake nazari a gameda yadda zamu cima burin da ya sanya smuka tura sojojin namu a Afghanistan, saboda yanzu babu tabbatas za'a iya cimma wannan buri.

Shi kuwa kakakin jam'iyar Greens a majalisar, Jürgen Trittin yana gain akwai sauran al'amuran da jawabin na Merkel bai tabo su ba. Misali yayi tambayar:

Shin me muka yi a Afghanistan. Shin muna kokari ne mu tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ko kuwa yamki muke kawai da yan tawaye. Shin menene burin siyasa da muke so cimma. Wane dalili ya sanya sojojin namu suke yakin, har suka rasa rayukan su. Har zuwa tsawon wane lokaci ne zamu ci gaba da zama a can.

Dangane da haka, Merkel tace sojojin zasu ci gaba da zama a Afghanistan muddin ana bukatar su a can. Abin dake da muhimmanci shine a sami damar mika alhakin tafiyarda kasar ga su kansu yan Afghanistan, abin da ma aka shirya fara shi a shekara ta 2011.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Yahouza Sadissou