1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayanin shugaban kasar Jamus game da rikicin zabe

July 21, 2005

Har ila yau dai, babu tabbacin ko za a gudanad da zabe a nan Jamus a cikin watan Satumba mai zuwa ko kuma a'a. Kome dai zai dogara ne kan irin shawarar da shuagaban kasa Horst Köhler zai yanke. Masu adawa da gudanad da zaben dai sun yi barazanar daukaka kara gaban babban kotun kundin tsarin mulkin kasa ta tarayya, idan aka rusa majalisa don shirya sabon zabe.

https://p.dw.com/p/Bval
Shugaban kasar Jamus, Horst Köhler.
Shugaban kasar Jamus, Horst Köhler.Hoto: AP

Ana nan dai ana ta rade-radi kan irin shawarar da shugaban kasa Horst Köhler zai yanke, game da rusa majalisar dokoki ta Bundestag don kira ga gudanad da sabon zabe a cikin watan Satumba mai zuwa, kamar yadda shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder da kuma mafi yawan `yan majalisar ke bukatar a yi.

Amma akwai wasu `yan majalisar kuma, da ke ganin cewa, kira ga rusa majalisar don gudanad da zabe shekara daya kafin takamaimaiman lokacin zaben, wato wata tabargaza ce. A ran 1 ga wannan watan ne, shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder, ya bukaci majalisar ta ka da kuri’ar amincewa ko kuma yin watsi da gwamnatinsa. Sai dai, wasu `yan majalisar na ganin hakan wani shiri ne da shugaban ya tsara don ya iya maido da lokacin zaben zuwa gaba da shekara daya. Werner Schulz, dan majalisa na jam’iyyar Greens na cikin masu adawa da manufar shugaba Schröder. A muhawarar da aka yi kafin a ka da kuri’ar a majalisa, ya bayyana cewa:-

„Abin da ke wakana yanzu haka a nan, wani shiri ne, kuma tabargaza ce. Wannan bukatar ka da kuri’ar yin amanna da gwamnatin ba ta kwarai ba ce. Farkon jumlarka ma, ya shugaban gwamnati, ba gaskiya ba ce. Ba ka sha’awar ganin an ka da kuri’ar amincewa da gwamnatinka. Abin da kake so ne ganin ka rasa rinjayi.“

A babi 68 na kundin tsarin mulkin kasar Jamus an bayyana cewa: idan shugaban gwamnati bai sami rinjayin masu yin amanna da gwamnatinsa ba, zai iya mika bukatar rushe majalisa ga shugaban kasa don a sanya lokacin gudanad da sabon zabe. Kamata ya yi dai, shugaban gwamnatin ya yi kokarin samun goyon bayan mafi yawa daga cikin `yan majalisar. Amma idan hakan ya gagagra, to dole ne a bai wa shugaban damar kiran wani sabon zabe.

Bisa halin da ake ciki yanzu dai, gwamnatin tarayya na da rinjayi a majalisa. Sai dai, wasu daga cikin `yan majalisar na jam’iyyarsa ta SPD, sun ki goyon bayan shirin nan na Agenda 2010 da ya gabatar, wanda ya tanadi yi wa ka’idodji da dama da suka shafi halin rayuwar jama’a garambawul. Sabili da hakan ne kuwa ya bukaci ka da kuri’a a majalisar. A cikin jawabinsa ga taron da majalisar ta yi a ran 1 ga wannan watan don tattauna wannan batun, shugaba Schröder ya bayyana cewa:-

„Idan muka yi la’akari da halin da ake ciki yanzu a wannan majalisar, kafin ma a yanke shawarar kiran sabon zabe ko kuma bayan haka, za mu iya ganin – ni dai na tabbatad da haka – cewa, ba ni da cikakken masu amanna da manufofi na, don in iya ci gaba da mulki kamar yadda babi 68 na kundin tsarin mulki ya tanadar.“

A karshen wannan muhawarar dai, `yan majalisa dari 4 da 44 daga cikin dari 5 da 59 ne suka ka da kuri’ar kin amincewa da gwamnatin shugaba Schröder. Kusan rabinsu kuma, `yan jam’iyyun gwamnatin ne dai da shugaban ke yi wa jagoranci.

To bayan sakamakon wanna kuri’ar da aka ka da ne, aka kai batun ga shugaban kasa Horst Köhler. Saboda shi ne a yanzu zai yanke shawara kan rushe majalisar ko kuma don gudanad da sabon zabe, ko kuma a’a.

To a nan ne fa ake ta jayayya har yanzu. Idan ya amince da bukatar da shugaba Schröder ya gabatar masa, ya rusa majalisar ya kuma tsai da ranar zabe, wasu `yan majalisar, kamar dai Wener Schulz, sun yi barazanar daukaka kara gaban babban kotun kundin tsarin mulkin kasa ta Karlsruhe. A nasu ganin dai, shugaban gwamnatin na da cikakken rinjayi a majalisar. Shi ya sa kuri’ar da aka ka da, wato magudi ne kawai da shugaban da maogoya bayansa suka tabka, sa’annan kuma suke wasa da hankulllan jama’a don cim ma burin son zucinsu.

Majalisar dokokin dai, ta taba samun kanta cikin irin wannan halin a cikin shekarar 1982. A wannan lokacin, shugaban gwamnatin tarayya Helmut Kohl, shi ma ya bukaci a gudanad da irin wannan zaben a majalisa. Duk da karar da wasu `yan majalisa suka dauka gaban kotun kundin tsarin mulkin kasa, ba su ci nasara ba. Sai da aka gudanad da sabon zabe.

Amma a wannan karon, ra’ayin alkalan kotun kundin tsarin mulkin ma ya bambanta.