1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BBOG ta bai wa Najeriya wa'adi

March 13, 2018

Kungiyar nan da ke fafutikar ceto 'yan matan Chibok a Najeriya ta zargi gwamnati da rashin kwarewa da kuma sakaci dangane sace 'yan mata 110 a shiyar arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/2uGpI
Nigeria Demonstration Bring Back Our Girls in Chibok
'Yan kungiyar Bring Back Our Girls a NajeriyaHoto: Reuters/A. Akinleye

Kungiyar nan da ke fafutikar ceto 'yan matan makarantar Chibok a Najeriya ta zargi gwamnatin kasar da abin da ta kira rashin kwarewa da kuma sakaci dangane da 'yan mata 110 da aka sake sacewa a shiyar arewa maso gabashin kasar.

Kungiyar ta Bring Back Our Girls, ta yi kaurin suna ne a fafutikar neman kubutar da 'yan matan Chibok 276 da kungiyar ta Boko Haram ta kwashe su kimanin shekaru hudu da suka gabata.

Ta dai bai wa gwamnatin Najeriya kwanaki bakwai na tabbatar da ceto 'yan matan Dapchi 110 da aka kwashe a watan jiya da ma na Chibok 112 da suka saura a hannun kungiyar Boko Haram.