1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beljiam ta ɗauki jagorancin karɓa karɓa na EU

July 1, 2010

Cikin yanayin rikicin siyasa Ƙasar Beljiam ta ɗauki jagorancin karɓa-karɓa na Ƙungiyar Tarayya Turai har tsawan watanni shidda

https://p.dw.com/p/O8MI
Beljiam ta ɗauki jagorancin EUHoto: DW

Yau ne ƙasar Beljiam ta ɗauki jagorancin karɓa -karɓa na Ƙungiyar Taraya Turai.

Wannan shine karo na 13 da Beljiam zata riƙe wannan muƙami dake juyawa ko wane watanni shida tsakanin ƙasashe membobin EU.To sai dai awanan karo mulkin ya zo a daidai lokacin da ƙasar ta faɗa cikin wani mummunan rikicin siyara tsakanin ´yan ƙabilar Flamand da masu amfani da halshen faransanci.

A yayin da yake jawabi bayan ɗaukar muƙamin, Firaminstan riƙwan ƙwarya Belijiam Yves Leterme cewa yayi:

"Za mu nemi sulhu game da dukkan wasu batutuwa da zasu taso.Zamu yi aiki domin ƙara kusanto ra´ayoyin ƙasashen EU.Burinmu shine mu ciyar da Ƙungiyar gaba"

Mahimman ƙalubalen dake gaban hukumomin Brussels a wannan jagoranci, sun haɗa da cimma daidaito wajen warware matsalar tattalin arzkin da ta addabi ƙasashen Ƙungiyar Tarayya Turai da kuma cigaban tattanawa domin faɗaɗa Ƙungiyar zuwa ƙarin wasu ƙasashe.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita:Umaru Aliyu