1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beljiyam ta dakatar da macin rashin tsoro

Kamaluddeen SaniMarch 26, 2016

Hukumomin Beljiyam sun bukaci al'umma da kada su shiga zanga-zangar nuna alhinin harin filin jirgin birnin Brussels a gobe lahadi sabili da rashin tabbas kan yanayin tsaro.

https://p.dw.com/p/1IKJl
Belgien Brüssel Jan Jambon und Yvan Mayeur
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Maeterlinck

A yayin da yake bayani a wannan Asabar Ministan cikin gidan Beljiyam Jan Jambon ya nemi masu machin da su dageshi har zuwa nan da wasu makonni don kauce wa abin da zai je ya zo.

Ministan ya kara da cewar: "Har yanzu daukacin kasar na cikin wani yanayin barazanar tsaro. Muna ci gaba da neman muhimman bayanai yanzu haka,. Wannan ne kuma dalilin da ya sa muke kira ga 'yan kasar da kada su yi maci a gobe. Maimakon haka a dageshi zuwa wani lokaci."

A makon nan ne dai 'yan kasar Beljiyum suka shirya wani gangami domin nuna takaicinsu kan harin da Kungiyar IS ta kai a filin tashin jiragen sama da tashar karkashin kasa na Brussels inda mutane da dama suka mutu tare da jikata sama da dari daya.