1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benin: An rantsar da sabon shugaban kasa

Rodrigue/Abdurrahman HassaneApril 6, 2016

An rantsar Patrice Talon a wannan Larabar a birnin Porto-Novo. Sai dai an gudanar da bikin ne ba tare da halartar shugabannin kasashen Afirka ba, saboda matsalar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/1IQTY
Benin Kandidat Patrice Talon vor der Stichwahl für den 16.März
Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Hakan ya auku ne saboda Shugaba Talon ya ce kasar tana fuskantar matsi na tattalin arziki don haka babu bukatar yin kashe -kashen kudade na ba gara babu dalili.

Patrice Talon tare da rakiyar mai dakinsa sun isa a babban filin kwallon kafa na Charles Degaulle na Porto Novo da ke a kudancin kasar da misalin karfe goma na safe inda ya sha rantsuwar kama aiki a gaban wakilai na jam'iyyun siyasa da jami'an diploamasiya na kasashen waje da kuma sarakunan gargajiya.

Sai dai babu ko daya daga cikin shugabannin kasashen Afirka da ya halarci bikin wanda aka yi ba kida ba alkariya babu wata kwarmniya saboda dalilai na yi tsumi da tanadi sakamakon matsi na tattalin arziki da kasar ke fuskanta. Ga Abinda Patrice Talon din ke cewa jum kadan bayan an kammala bikin rantsar da shi:

"Ina mai furta kallamun cewar abin da muka yi a yau , zai iya zama wata alama ta sake farfadowar kasarmu,Al'ammura ba sa tafiya ko kadan a kasarmu amma shawo kan lamari ba zai gaggara ba, abin da ke jiranmu yana da girma amma dai za mu iya."

Westafrika Benin Unterstützer des Präsidentschaftskandidat Patrice Talon
Bukukuwan murna a BeninHoto: Reuters/C. P. Tossou

Patrice Talon dan kasuwa kana attajirin mai kudi wanda ake yi wa la'akabi da sunan sarkin audiga dan shekaru 57 da haifuwa wanda ya samu goyon bayan jam'iyyun siyasa 24 ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na Benin da kishi 65 cikin dari na kuri'un da aka kada a gaban abokin takararsa tsohon firaminista Lionel Zinsou..

Shakka babu wannan sabon salo na bikin rantsar da shugaban kasar shi ne irinsa na farko da ya wakana a yankin yamacin Afirka wanda wasu na kusa da sabon shugaban kasar suke yi marhabin da hakan .Dieudonne wani na hannun daman shugaba Patrice Talon ne

Ya ce "da tsohuwar al'adar da aka saba da ita tun a ranar ta farko ta rantsuwar kama aikin an fatataki kudaden kasa mu ba wannan ya kawo mu abin da ke a gaban shugaban kasar yana da yawa don haka ba za mu yi amfanin da kudaden kasar cikin irin wannan hanya ba za mu sakasu cikin hanyoyi masu kyau."

Bayan shan rantsuwar kama aiki Talon ya yi ban hannu na aiki da tsohon shugaban kasar mai barin gado Thomas Bonni Yayi wanda ya yi wa'adi biyu na mulki na tsawon shekaru goma.

Benin Präsidentschaftskandidat Patrice Talon
Shugaba Talon gabanin tantsar da shiHoto: Reuters/C.P. Tossou

Wanda kuma tsohon amini ne na Talon kafin su raba gari, har Boni ya nemi ya kule Talon a gidan kurku duk da cewar shi ne ya rika bashi kukdaden yin farfagadi amma ya samu ya arce zuwa Faransa inda ya yi hijira shekaru da dama kafin ya dawo Bennin watannin kalilan kafin zaben,

Sai dai sabannin didimar da aka sha a bukukuan rantsar da tsohon shugaban kasar watau Boni Yayi a shekarun 2006 dakuma 2011 a wannan jikon an yi bukukuwan ne cikin sauki kamar yadda daraktan farfagandi sabon shugaban Sacca Lafia ya bayyana

"Abin da kasarmu za ta fi ba da fifiko a kai shi ne aiki, da kuma ci gaba muna cikin wani hali na matsi a cikin irin wannan yanayi kuma babu kashe-kashe dukiyar kasa, shi ya sa ma ba mu gayyaci ko da daya daga cikin shugabannin kasahen Afirka ba."