1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benitta Ferroro da Cecilia Sarkozy a Lybia

July 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuFj

Komishinar hulɗoɗi da ƙetare ta ƙungiyar tarayya turai, Benita Ferrero waldner, tare da rakiyar matar shugaban ƙasar France Cessilia Sarkozy, a yanzu haka,su na Lybia, inda su ke tantanawa da hukumomin wannan ƙasar a game da nas-nas ɗin nan na ƙasar Bulgaria guda 5, da doktka ɗaya na Palestniu, da su ka samu afuwa, bayan hukuncin kissan da kotu ta yanke masu a dalilinda zargin da a kayi masu, na yaɗa ƙwayoyin cutar Sida, ga ɗaruruwan yaran ƙasar Lybia.

Tawagar matan 2, na buƙatar hukumominTripolie, su yi belin wannan likitoci ta la´akari da afuwar da su ka samu.

Gobe idan Allah ya kai mu, shima shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy, zai issa ƙasar ta Lybia, domin ciga da lallashin shugaba Ƙhadafi, ya amince da mayar da wannan likitoci a ƙasashen su, na asuli.