1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bernd Neumann, ya kawo ziyara a gidan rediyon Deutsche Welle.

YAHAYA AHMEDJune 9, 2006

A ziyarar da ya kawo wa gidan rediyon Deutsche Welle a nan birnin Bonn, ƙaramin ministan al'adu da kafofin yaɗa labarai na tarayyar Jamus, Bernd Neumann, ya yi wata doguwar fira da cif editan gidan rediyon, Miodrag Soric, inda ya zayyana matsayiin ma'aikatarsa a fagen al'adu na Jamus. Ga dai gundarin firar da suka yi.

https://p.dw.com/p/BvTX
Ƙaramin ministan kula da al'adu da kafofin yaɗa labarai na tarayyar Jamus, Bernd Neumann.
Ƙaramin ministan kula da al'adu da kafofin yaɗa labarai na tarayyar Jamus, Bernd Neumann.Hoto: picture-alliance/ dpa

A ziyarar da ya kawo wa gidan rediyon Deutsche Welle da ke nan Bonn, ƙaramin ministan al’adu da kafofin yaɗa labarai, Bernd Neumann, ya tattauna da shugabannin wannan gidan rediyon a kan batutuwan da suka shafi harkokin yaɗa labarai a cikin wannan zamanin, da kuma irin ƙalubalen da kafofin yaɗa labarai ke huskanta wajen gudanad da ayyukansu.

A cikin wata doguwar firar da ya yi da cif editan Deutsche Welle, Miodrag Soric, Bernd Neumann, ya nuna bambancin da akwai tsakanin ma’aikatarsa da sauran jihohin tarayya, waɗanda kawo yanzu, su ne ke kuma kula da batutuwan da suka shafi al’adu.:-

„Harakar al’adu ba a hannun jihohin tarayya kawai take ba. Babu shakka, jihohin na taka muhimmiyar rawar gani a batutuwan da suka al’adunsu. Amma idan aka yi la’akari da ƙasar Jamus gaba ɗaya, nan ma kamata ya yi, a sami wata kafa guda ɗaya, wadda za ta dinga wakilcinta a harkokin al’adun. A nan ne dai hukumar tarayya ke da nata angizon. Ka ga dai kamar a babbar birnin tarayya Berlin, duk wasu harkokin al’adu, saboda sun shafi kasa ne gaba ɗaya, to a hannun ma’aikatarmu take. Ba kawai al’adu ba, ni kuma minista mai kula da kafofin yaɗa labarai. Sabili da haka, harkokin Deutsche Welle ma, ta shafi ma’aikatarmu. A lokacin aiki na dai, zan yi ƙoƙarin ganin cewa, ba a bar kafofin yaɗa labaran ma a baya ba.“

Ministan dai, ya ƙara bayyana cewa, shi ne farkon ɗan siyasar da aka taɓa naɗawa a wannan muƙamin. Sabili da haka, abin da zai bambanta aikinsa da na takwarorinsa da suka riga shi riƙe muƙamin, shi ne, irin ƙoƙarin da zai yi wajen ganin cewa a huskar siyasa ma, kafofin za su iya dogara kan wani wanda ya ƙware a wannnan fannin don kare maslaharsu.

Game da batun tsauraran matakan tsimin da gwamnatin tarayya ke ɗauka, waɗanda babu shakka, suna shafan kasafin kuɗin da ake ware wa kafofin yaɗa labarai kamarsu Deutsche Welle, ministan ya bayyana cewa:-

„Ai matsalar ba daga ɓangaren gwamnatin tarayya take ba. Idan aka dubi kasafin kuɗin da gwamnatin tarayya ta ware wa kafofin yaɗa labarai, za a ga cewa, babu wani ragi da aka yi a cikin ’yan shekarun bayan nan. Amma, duk inda aka sami ragowar kuɗaɗe, sai ka ga cewa, matsalar daga hukumomin jihohi suke. Abin alfahari a nan dai shi ne: a cikin yarjejeniyar da muka ƙulla ta kafa wannan gwamnatin haɗin gwiwa, mun yarje kan cewar, kuɗaɗen da za a kashe kann al’adu, ba sun tafi ba ke nan. Wato zuba jari ne, wanda kuma, za a ci moriyarsa nan gaba.“

Game da batun tuntuɓar juna kuwa, da gwamnatin tarayya ke ta nanata muhimmancinsa tamkar wani jigo ne da ta sanya a gaba, ministan ya ce tattaunawa da duniyar musulmi a cikin wannan zamanin, na da muhimanci ƙwarai da gaske. Kamata ya yi a tinkari wannan batun a huskar siyasa da kuma na al’adu. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Ya kamata mu fara tattaunawa da juna a fagen siyasa, don mu iya cim ma fahimtar juna. Wannan kuwa, a nan cikin gida Jamus ya kamata mu fara shi. Ya kamata mu yi ƙoƙarin fahimtar baƙi da ke zaune a nan, sa’annan kuma mu sami damar bayyana musu, yadda halin rayuwarmu yake. Na yi imanin cewa, wannan abu ne mai yiwuwa, kuma yana da muhimmanci a aiwatad da shi.“