1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ajje makamai a yammancin Cote D´Ivoire

July 27, 2006
https://p.dw.com/p/Buow

A cen ma Cote d´Ivoire, an yi bikin ajje makamai a yankin Guiglo da ke yammacin ƙasar, inda ɗaruruwan matasa yan ƙungiyar FRGO masu goyan bayan shugaban ƙasa Lauran Bagbo, su ka miƙa makamai masu yawa, ga Praministan riƙwan ƙwarya Charles Konnan Banny.

Shugaban matasan FRGO Denis Maho Gofliei, ya bayana wa hukumomi cewar ƙungiyar sa, ta ɗauki wannan mataki domin bada haɗin kai ga yunƙurin samar da zaman lahia, da kuma shirya zaɓe cikin kwanciyar hanakali.

Denis ya yi kira ga sauran ƙungiyoyin sa kai, da na yan tawaye da su yi koyi da FRGO.

A jimilce ƙungiyar ta miƙa makamai 300 da su ka haɗa da manya- manya guda 50.

Masu kulla da al´ammura a ƙasar Cote D´Ivoire,sun ce makaman da ƙungiyar ta miƙa ba su taka kara sun karya ba, indan a ka auna, da yawan makaman da ta mallaka.

An ƙiyasta cewar yawan matasan da su ka shiga yaƙin sa kai, a yammacin Cote d´Ivoire, ya kai a ƙalla dubu 10.

Majalisar Dinkin Dunia ta tanadi tsari na musamman na basu yan kuɗaɗen girka sana´a, a matsayin hurhure, da makaman da su ka ajje.