1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin aláda ta Noruz kasar Iran

March 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4d

Yayin da kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya ke dab da yanke kudiri a game da shirin Nukiliyar ƙasar, a hannu guda alúmar Iran ɗin na kokarin kawar da hankulan su daga batun nukiliyar, inda suke shirin fara hidima ta tsawo makwanni biyu na bikin sabuwar shekara. A yau ne dai ƙasar Iran din ke bikin Noruz wanda ya zo dai dai da ranar da wakilan dundundudn a kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya, tare da kasar Jamus ke kokarin cimma yarjejeniya a kan wani tsarin jadawali, da zai shawo kan Iran ta yi watsi da shirin sarrafa makamashin Uranium. Ko da yake alúmar Iran din na baiyana damuwa a game da makomar ƙasar idan aka kakaba ma ta takunkumi, a yanzu bikin zagayowar shekarar ce babban abin da suka maida hankali a kai.