1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin al´adu da waƙoƙin Afirka a Würzburg

June 18, 2009

A kwanakin baya ne a birnin Würzburg na nan Jamus aka gudanar da bikin waƙoƙi na Afirka karo na 21.

https://p.dw.com/p/ISqa
Hoto: www.africafestival.org

Wannan bikin dake zama wani bikin waƙoƙi da na al´adun Afirka mafi girma a nahiyar Turai, a wannan karon ya samu halarcin makiɗa da mawaƙa kimanin 250 daga kowane sashe na Afirka cikinsu kuwa har da Oumou Sangare da Salifou Keita mashahuran mawaƙa daga ƙasar Mali. Hakazalika baƙi sama da dubu 100 suka shaida bikin na bana.

Wannan bikin dake zama irinsa mafi girma a nahiyar Turai baki ɗaya a bana ya cika shekaru 21. Ya dai samu halarci mashahuran mawaƙa daga ko-ina cikin Afirka sai kuma manyan baƙi da suka haɗa da jakadan Afirka Ta Kudu a Jamus Sonwabo Funde. Wata mai suna Mona ta na ɗaya daga cikin masu sha´awar irin waɗannan bukukuwa na Afirka ta yi nuni da cewa.

“Suna Mona na zo wannan wuri ne don in more daga waƙoƙi da abinci iri daban daban da aka baje kolinsu a nan. Hakazalika yawan mutanen da suka haɗu a nan wani abu ne da ya burge ni ƙwarai da gaske.”

Bildergalerie Africa Festival 2009
Hoto: Horst A. Friedrichs

Ko shakka babu abu mafi ban sha´awa ga duk mahalarci wannan bikin shi ne kawai ya saje cikin cunƙoson jama´a dake kai komo a gun wannan biki na garin Würzburg. Babu maƙawa duk wanda ya halarci bikin zai sadu da mutane daban daban. Ga dai lafazin wasu Jamusawa mahalarta wannan biki.

“Muna jin daɗin wannan bikin kasancewa mutane daga ko-ina cikin duniya sun a nan wurin. Wannan wani yanayi mai ban sha´awa kuma mai burgewa. Muna morewarmu kuma mun samu yanayi mai kyau.”

“Ina zuwa nan wurin ne saboda kasancewarsa wani dandali na musayar al´adu kana kuma za ka samu sukunin zantawa tare da koyan wasu abubuwa daga ´yan´uwanmu maza da mata daga nahiyar Afirka, musamman bisa la´akari da tatsuniyoyi da kuma fasahohin da suke nunawa. Waɗannan fasahohin da sassaƙa sun ɓace a nan Jamus baki ɗaya. Abin sha´awa ne idan ka zo ka ga waɗannan abubuwa a nan."

Wata mai suna Vanessa daga ƙasar Madagaska na ɗaya daga cikin masu baje kolin kayan sassaƙa a rumfunan da suka haya a gun bikin. Ta yi nuni da irin gagarumar nasarar da suke samu.

“E, tabbas Jamusawa na sha´awar kayakin sassaƙa. Suna matuƙar sha´awar al´adun Afirka da ma na wasu nahiyoyin. Suna daraja su ƙwarai da gaske. A saboda haka suke son kayan sassaƙa da sauran kayakin saƙa da suke amfani da su wajen adon ɗaki. Da yake ba su da wata ƙasa da suka yiwa mulkin mallaka ya sa suna ɗokin irin salon rayuwa a Madagaska da ma Afirka baki ɗaya.”

Bildergalerie Africa Festival 2009
Thandiswa MazwaiHoto: Bugs Steffen

Abin da ya fara ɗaukar hankali a bikin na bana shi ne wasan kiɗe-kiɗe na ƙaddamar da bikin inda aka nuna bangirma ga maraigayiyya Mariam Makeba wadda ake yiwa laƙabi da Mama Afirka wadda ta rasu a cikin watan Nuwamban bara tana da shekaru 76 a duniya. Ga Thandiswa Mazwai mai rubuta waƙoƙi, har yanzu Mariam Makeba na matsayin kyakkyawar abar koyi a jerin mawaƙan nahiyar Afirka. Ita dai Thandiswa Mazwai na ɗaya daga cikin mashahurai a fagen al´adun Afirka Ta Kudu. Tana haɗa waƙoƙin gargajiya da kiɗe-kiɗe zamani. Kamar Marima Makeba, ita ma tana waƙa ne a cikin harshenta na asali wato Xhosa.

“Yana da muhimmanci a gareni domin da wannan harshe na Xhosa ne kaɗai na ke iya yin waƙa. Na yi imani cewa waƙa wana abu ne da ke ci-gaba da wakana a kullum. Ba abu ne day a fara yanzu ba, ya samo asali ne tun zamanin kakan kakanni kuma zai ci-gaba har bayan mu. Kuma harshe na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke tabbatar ad wanzuwar tarihi da al´adu da kuma darussan da muka gada daga iyaye da kankanni. Yana da muhimmanci ƙwarai da gaske.”

Bildergalerie Africa Festival 2009
Oumou SangareHoto: Bugs Steffen

Ganin yadda mata mawaƙa daga Afirka suka taka rawar gani a gun bikin ana iya cewa wani dandali ne da mata suka nuna bajimta. Oumou Sangare shararriyar mawaƙiya daga Mali na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Afirka da suka halarci wannan biki. Ta kuma shahara a matsayin mai ƙwatowa mata ´yanci. A gun bikin na Würzburg ta ƙaddamar da sabon faifayenta mai taken Wele Wele Wintou dake yaƙi da auren dole.

“Kiɗan Wele Wele Wintou na matsayin kira ne ga iyaye domin su daina yiwa ´ya´yansu auren dole. Suna karɓar maƙudan kuɗaɗe, haka kuwa bai dace ba. Ina roƙon irin waɗannan iyaye da sun san cewa aure ma da aka yi bisa soyayya ya kan fuskanci matsaloli balantana auren dole. Na yi murnar ganin yadda matasa ke nuna sha´awarsu kan wannan batu.”

Ban da kiɗe-kiɗe an kuma taɓo batun siyasa da zamantakewa a gun bikin na Würzburg musamman game da halin da zabiya ke ciki a Afirka, waɗanda wasu al´ummomin ke danganta zabiya da maita. Sanon Fabere wanda zabiya ne daga ƙasar Burkina Faso ya ce tun yana a firamare ake nuna masa wariya. Yanzu haka dai ya kafa wata ƙungiyar shigar da zabiya cikin harkokin yau da kullum na jama´ar ƙasa.

“Na sha wuya a firamare domin ´yan makarantarmu ba su san zabiya ba. An yi ta yawaita tambaya ta ko ni ma daidai na ke da sauran yara musamman game da hazaƙa. Sa´o´i na su kan jimi rauni don su ga ko ni ma jini na ja ne kamar na su. Wasu daga cikinsu kuma na tsoro idan suka ga yaro ƙarami kamarsu amma fari.”

Bildergalerie Africa Festival 2009
Hoto: Diego Ravier

Ɗaya daga cikin mashahuran maaƙan Afirka da shi ma ke fama da wannan matsala ta ´yan zabiya shi ne Salif Keita ɗan ƙasar Mali. A farkon wannan shekara ya ƙaddamar da wani shirin tallafi don samar da man shafawa da kuma rigunar kariya na musamman ga zabiya waɗanda fatarsu ba ta da wata kariya daga zafin rana.

Da dai kiɗa Sali Keita aka kammala bikin na bana a Würzburg sai kuma a baɗi idan mai duka mai komai ya kaimu.

Mawallafa: Carine Debrabandère/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal