1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin Baje Kayan Tarihin Masar

November 4, 2004

A jiya laraba ne shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak suka gabatar da bikin baje kayan tarihin kasar Masar a birnin Bonn

https://p.dw.com/p/Bveu
Bikin baje kayan tarihin kasar Masar
Bikin baje kayan tarihin kasar MasarHoto: AP

Har yau duniya na mamakin wannan sarki da aka yi a kasar Masar, fir’auna Tutanchamun, wanda ya kawo babban canji ga daular Masarawa ake kuma tababa a game da musabbabin mutuwarsa. Wannan mamaki da doki da mutane a dukkan sassa na duniya ke yi domin nakaltar ire-iren kayayyakin tarihin fir’aunonin na kasar Masar, wata manufa ce da ka iya taka muhimmiyar rawa wajen samar da kusanta da fahimtar juna tsakanin jama’a, a cewar shugaba Hosni Mubarak da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder a lokacin kaddamar da bikin baje kayan tarihin a daya daga cikin gidajen kayan tarihi na birnin Bonn a jiya laraba. Duk wanda ya waiwayi baya ya nakalci tarihin mutan-da, ba shakka zai koyi darasin da ka iya zama gargadi a gare shi wajen tafiyar da harkokin rayuwarsa ta yau da kullum, in ji shugaban gwamnati Gerhard Schröder, wanda kuma ya kara da cewar:

"Bisa ga ra’ayi na musayar al’amuran al’adu abu ne dake taka muhimmiyar rawa a manufofin siyasa. Domin kuwa ta nakaltar al’adun juna ne za a kai ga fahimta da kuma kauce wa yanke hukunci ba a bisa basira ba."

Kasashen Turai na sha’awar al’adu da tarihin fir’aunonin Masar in ji shugaban gwamnatin na Jamus. A nasa bangaren shugaba Hosni Mubarak yayi nuni ne da cewar babban muradin dukkan sassan biyu shi ne kyautata fahimtar juna tsakanin Jamusawa da Masarawa. Kuma bitar tarihin al’adu kan taimaka bisa manufa. Mubarak ya kara da cewar:

"Makasudin wannan bikin baje kayan tarihin shi ne kasancewar kayan fasahar al’adu tamkar wata gada ce dake sadarwa tsakanin jama’a, kuma tarihin fir’aunonin Masar na taka gagarumar rawa a neman kusantar junan da ake yi tsakanin Musulmi da Kristoci da Yahudawa saboda dukkan addinan na da nasaba da wannan tarihi."

Za a dai yi tsawon watanni shida ana baje kayan tarihin a nan birnin Bonn.