1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin baje kolin motoci a Frankfurt

September 20, 2007

Motoci masu rangwamen kudi su ne suka fi daukar hankalin maziyarta a zauren bikin bajen kolin motocin na bana

https://p.dw.com/p/BtuY
Bikin baje kolin mota a Frankfurt
Bikin baje kolin mota a FrankfurtHoto: DW

Kusan dukkan kamfanonin kera motoci, a halin yanzun, sun ankara da muhimmancin kera motoci ‘yan kanana masu rangwamen farashi na kasa da Euro dubu 10. Misali motar Aygo kirar kamfanin Toyota, wanda kudinsa ya kama Euro dubu tara da 350. To sai dai kuma kudin motar kan yi sama daidai da ire-iren kayan alatun da mutum ke neman ganin an kawata masa motar da su, a baya ga abubuwan da aka tanadar mata tun farko kamar rediyo da rikoda.

Shi ma kamfanin Ford ya kira wata ‘yar karamar motar mai take Ka Studenta, wadda kudinta ya kama euro dubu takwas da metan. To sai dai kuma ba dukkan masu ziyartar zauren bikin baje motocin ne ke bayyana gamsuwarsu da motar Ka Student kirar kamfanin na Ford ba.

“Motar tayi tsada idan an kwatanta da amincinta, kamar yadda nike gani. Bayan shekaru biyu zaka ga wannan fentin da aka yi mata ta ciki ta fara karcewa, wannan abu ne da ba shakka game da shi. A saboda haka zan gwammace yin karin euro dubu daya in samu wata amintacciyar mota. Domin wannan kyal-kyal banza ce kawai.”

Amma fa ba motar Ford Ka din ce tafi kowace rafusar farashi a zauren bikin na bana ba, akwai motoci kirar Citroen ko Lada da Dacia, wadanda farashinsu ya gaza euro dubu takwas. To sai dai kuma, kamar yadda Hausawa su kan ce: Ba girin-girin ba, tayi mai. Wato muhimmin abu dangane da wadannan motoci, ba kawai arahar farashinsu ba, sai dai yawan mai da suke aiwatarwa. Domin kuwa galibi yawan mai da ire-iren wadannan motoci ke aiwatarwa ya kan sanya su fi manyan motoci tsada. A dai halin da ake ciki yanzun kamfanonin motocin sun dukufa ka’in da na’in wajen kira kananan motoci masu rangwamen farashi da kuma kayyade yawan mai da suke aiwatarwa. A lokacin da yake bayani game da haka Martin Winterkorn shugaban kamfanin Vogswaja cewa yayi:

“Ba shakka nan gaba za a samu motoci da farashinsu ya gaza euro dubu 10 a nahiyar Turai, daidai irin tanadin alatun da aka yi musu, kuma a yanzu haka mun fara tunanin kera motoci, wadanda farashinsu bai zarce euro dubu shida ba, daidai da bukatun jama’a.”

Akwai wasu rahotannin dake cewar tuni kamfanonin Toyota da General Motors suke kan hanyar kera motocin da farashinsu bai kai dalar Amurka dubu hudu ba. Amma mota mafi rafusa a duniya, ita ce wadda kamfanin motocin Tata na Indiya ke da niyyar fitarwa kasuwa shekara mai zuwa akan farashi na euro dubu daya da dari takwas.