1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin buɗe wassanin ƙwallon ƙafa na duniya

June 11, 2010

Mawaƙa na duniya sun cashe a kaɗe -kaɗen share fagen na cin kofin duniya na ƙwallon ƙafa a Afirka ta ƙudu

https://p.dw.com/p/No0s
Shakira zabayar wassaninHoto: AP

Nan gaba ƙaɗan ne inda a juma aka shirya buɗe gasar cin kofin duniya na ƙwallon ƙafa a Afirka ta kudu. Gasar wace ita ce ta farko da ake yi a Afirka tun da marecen ranar Alhamis mayan mawaƙa na duniya suka share fagen wassanin da kaɗe-kaɗe  a filin wassanin na Orlondo da ke Saweto a gaban sama da mutane dubu 35 yan kallo galibi yan yawon buɗe ido, tare da hallarta shugaban ƙasar na Afrika ta kudu Jakob Zuma da kuma Serpp Blater shugaban ƙungiyar wassanin ƙwallon ƙafa na FIFA

Shaharariyar mawaƙiyar nan yar ƙasar Kwalanbiya Shakira ita ce ta buɗe labulen kaɗe kaɗen.

A waje guda kuma an bada rahoton wata tataɓakunnen Nelson Mandela Zenani`yar shekaru 13 da haihuwa  ta rasu a haɗarin mota akan hanyarta ta komawa gida bayan wassanin.

A karawar farko ta wassanin na yau Afrika ta ƙudu za ta kece raini tsakaninta  da Mexiko  sanan Faransa ta yi karon battan ƙarfe da ƙasar Yurigai

Mawallafi  :Abdourahamane Hassane

Edita         : Abdullahi Tanko Bala