1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin bude gidan tarihin Holocaust a Kudus

March 15, 2005

Kimanin shuagabannin kasashe 40 ne ke halartar bikin bude gidan ajiye kayan tarihin ta'asar Holocaust a birnin Kudus

https://p.dw.com/p/Bvck
Gidan ajiye kayan tarihin Holocaust a Kudus
Gidan ajiye kayan tarihin Holocaust a KudusHoto: AP

Daga cikin kayayyakin da aka baje a gidan ajiyr kayan tarihin na karkashin kasa a birnin Kudus domin tunawa da ta’asar kisan kiyashin nan ta Holocaust da Yahudawa suka fuskanta a hannun ‚yan nazinhitler har da wata ‚yar tsana ta wata yarinyar da ‚yan nazi suka kashe iyayenta. A lokacin da yake bayani game da haka Avner Schalev, darektan gidan ajiyen tarihin ta’asar ta Holocaust nuni da yai da cewar:

Yarinyar ta rika watangaririya da wannan ‚yar tsana kuma bayan murkushe ‚yan nazin ‚yar tsanar ta zama wani muhimmin abin dake tunasar da ita game da iyayenta. Bata rabu da ‚yar tsanar ba sai bayan da ta girma ta kuma rubuta mata wasika tana mai cewar tsawon rayuwata kin kasance mai debe ni kewa a madadin iyayena, amma a yanzun lokaci yayi da zan yi bankwana dake in mika ki zuwa ga hannun da mutanen da a hakika baki san su ba, domin ki rika ba su tarihina. Ni kan nuna wa mutane wannan ‚yar tsanar da wasikar tare da ba su labarin matar, saboda wannan wani lamari ne mai ban ta'ajibi.

Gidan ajiye tarihin na ta’asar Holocaust mai suna Yad Vashem yana da tsawon mita 200 a wata suffa mai kusurwa uku. Kai tsaye mutum na iya hangen dukkan bangarorin ginin da wuraren da aka baje kayan tarihin dama da hagu. An tsara ginin ne ta yadda maziyarta zasu yi bitar tarihin dakidaki. Tarihin ya fara tun daga tushen ta’asar har ya zuwa karshen yakin duniya na biyu a shekarar 1945. kuma a karshe mutum zai fito daidai gaban tsaunin birnin Kudus domin zama martanin Isra’ila akan ta’asar Holocaust. A lokacin da yake bayani darektan gidan ajiye kayan tarihin na Holocaust Avner Schalev karawa yayi da cewar:

A karo na farko an gabatar da wani yunkuri na amfani da fasaha wajen bayanin abubuwan da gidan tarihin ya kunsa, tun farko har ya zuwa karshen ta’asar Holocaust. Daruruwan masu fasahar zuka ba da gudummawarsu wajen tsara wannan gini a karkashin kasa tare da binciken ta bakin mutanen da suka shaidar da ta’asar, wadanda aka baje hotunansu, tamkar sune ke ba da tarihinsu.

Manufar gidan tarihin dai, kamar yadda Avner Schalev ya nunar shi ne domin tunasarwa da kuma gargadin fuskantar irin shigen wannan ta’asa nan gaba.