1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin cika shekaru 60 da ƙaddamar da ´yancin bani Adama

Sadissou YahouzaDecember 8, 2008

`Yancin bani Adama ya cika shekaru 60 da ƙaddamarwa , shin ina aka kwana ? An ci nasara kokuma ja da baya aka yi?

https://p.dw.com/p/GBse
Dukan ´yan Adam daidai suke da ´yanciHoto: dpa


10 ga watan Desember na shekara ta 1948 , 1o ga watan Desember na shekara ta 2008, a kwana a tashi ,yau shekaru 60 kenan ciccip da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da dokar kare ´yancin bani adama a yayin zaman taron da ta shirya a birnin Paris na ƙasar France.

ƙudurin na Majalisar Ɗinkin Duniya, yayi amfani da dokar ƙasar France ta 1789 wadda ta tanadi hanyoyin kare ´yancin jama´a da kuma dokar samar da ´yancin kan ƙasar Amurika ta 1776.

Ƙasashe 58 wanda a lokacin ke matsayin membobin Majalisar Ɗinkin Duniya, suka ƙirƙiro wannan ƙuduri da zumar riga kafi ga ɓarkewar yaƙe-yaƙe, kamar yaƙin duniya na ɗaya da na biyu, da kuma kissan kiyasun da ´yan Nazi a nan Ƙasar Jamus suka yiwa bani yahudu.

Elenaor Roosvelt itace Majalisar ta dorawa yaunin karanta ayoyin da dokar ta tanada, inda da ta fara da share fage tare da cewa:

" ta la´akari da cewar dukan ƙasashen duniya sunyi baki guda a game da wajibcin kare haƙƙoƙin jama´a ta hanyar nuna adalci da ´yanci tsakanin ko wane mahaluki,ƙasashe membobin Majalisar Ɗinkin Duniya, sun yanke shawara rattaba hannu akan ƙuduri da zai tabbatar da wannan yanci."

Kudurin na Mjalisar Ɗinkin Duniya ya ƙunshi ayoyi fiye da 30 to saidai ta farko daga cikin su ke matsayin jagora.

" Ayar doka ta ɗaya,dukkan ´yan adam na da ´yancin iri ɗaya tun daga ranar aihuwa,babu banbanci ko fifiko tsakanin wane ko wance".

To saidai ayar tambaya nan itace shin a zahirin gaskiya mine tasirin wannan dokoki na Majalisar Ɗinkin Duniya ?

A cewar Heiner Bielefeldt shugaban hukumar kare haƙƙoƙin bani adama ta ƙasar Jamus, babu shakka an samu cigaba ta fannin kare ´yancin jama´a to amma har yanzu da sauran rina kaba.

" Har yanzu ana cigaba da take haƙƙoƙin jama´a , kussan babu wani cenji, idan aka dubi yanayin da duniya ke ciki, to amma an samu cigaba ta fannin girka kafofin ƙasa da ƙasa na gwagwarmayar ƙwato ´yancin bani adama."

Duk da cewar ba a cimma buri ba, amma babu shakka akwai Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da suka duƙufa domin ganin zahirin ´yancin bani adama ya tabbata.

Ƙasashe membobin Majalisar Ɗinkin Duniya,sun rattaba hannu a kan yarjejeniyoyi wanda suka haɗa da yarjejeniyar shekara ta 1979 wace ta haramta nuna wariya ga ´ya´ya mata, da ta 1984 wadda ta haramta ƙuntatawa ɗan adama ta hanyar duka da makamanta ta, sannan a shekara ta 1990 Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙadamar da ´yancin ƙananan yara, sai kuma Kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta manya leffika masu nasaba da take haƙƙoƙin jama´a da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙirƙiro a shekara ta 1998.

A cewar Kjaerum Morton shugaban hukumar kare manyan ´yancin bani adama a Ƙungiyar Tarayya Turai, wannnan ba ƙaramin cigaba ne aka samu ba.

"A shekara ta 1990,muna da Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama guda 10 rak, amma yanzu akwai fiye da 100 kuma mafiyawan su na da rassa a ƙasashen ƙetare, saboda haka batun kare haƙƙoƙin bani adama daga TUrai ya yadu a ko ina cikin duniya , a sakamakon hakan , zaka ga kotuna da magabata suna takatsantsan da batun da ya shafi ´yanci fiye da shekarun baya."

A ƙasashen Afrika kamar sauran ƙasashen duniya, Ƙungiyoyin fara hula masu gwagwarmar kare haƙƙoƙin bani adama ,sun taka rawar gani, saidai don cimma burin da aka sa gaba, Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsara ɓullo da wani saban shiri, albarkacin bikin cikwan shekaru 60.

Wannan shiri ya tanadi faɗakar da jama´a, a ko ina cikin duniya a game da hanyoyin koyan kare haƙƙoƙin bani adama.