1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin cikwan shekaru 50 da samun yancin kan Ghana.

March 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuQO

Yau ne al´ummar ƙasar Ghana ke bikin cikwan shekaru 50, da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Britaniya.

Rahottani daga birnin Accra, sun nunar da cewa, tun wajejen ƙarfe 10, na sahiyar yau, dubun dubbunan jama´a, su ka fara tururuwa zuwa babban filin da aka fi sani da suna, dandalin yancin kai, domin gudanar da shagulgulla.

Shugabanin ƙasashen Afrika 12, su ka halarci wannan buki, domin karrama yancin kan ƙasar farko ta Afrika kudancin Sahara.

Shugabanin sun haɗa da Olesegun Obasanjo na Nigeria, Tabon Mbeki na Afrika ta kudu , Robert Mugabe na Zimbabwe , Amadu Tumani Ture na Mali, da kuma Lauran Mbagbo na Cote d´Ivoire.