1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin hadin kan kasar Ivory Coast

July 30, 2007

:A karon farko cikin kusan shekaru 5 shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ya kai ziyara kudancin kasar,tsohon yankin da yan tawaye ke rike da shi a baya.Gbagbo ya kai wannan ziyara ce don halartar bukukuwan sake hadewawar kasar,da ajiye makamai da tsoffin yan tawayen zasuyi,a wani sabon yunkuri na karfafa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimmawa a watan Maris.

https://p.dw.com/p/Btut
ivory coast
ivory coast

Shugaban na kasar Ivory Coast ya samu kyakkyawar tarba a birnin Bouake daga tsohon shugaban yan tawaye Guilaume Soro wanda aka nada firaministan sabuwar gwamnatin kasar karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar.

Su dai shugabannin biuy suna bukatar ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya na aka sanyawa hannu a kasar Ivory Coast,shine kakakin Guillaume Soro.

Shugabani da suke halartar taron sun hada da Blaise Campaore na Burkina Faso da Thabo Mbeki na ATK da shugaban kasar Ghana kuma shugaban AU John Kufour,Abdullahi Wade na Senegal,Faure Gnasingbe na Togo Amadou Toumani Toure na Mali da Yayi Boni na Benin

Birnin Bouake shine hedkwatan tsohuwar kungiyar yan tawaye ta New Forces wacce ke rike da yammacin kasar na kusan shekaru 5.

Taron wanda aka shirya musamman don hade kan kasa da kuma kona makamai wanda shine alama ta farko na kwance damarar yaki a yammacin kasar.

Kakakin na kungiyar NF ya kuma ce an dauki matakan tsaro yadda ya kamata”matasa na gudanar da harkokin sun a yau da kullum kamar yadda ya kamata hakazalika yanayin zamantakewa tsakanin alumma na tafiya daidai kamar yadda ya kamata2

Akwai kusan dakarun yan tawaye 42,500 da sojojin gwamnati 5,000 da kuma sojojin sa kai 12,000 magoya bayan Gbagbo da za’a kwancewa damara a yau.

Yanzu haka dai jamian tsaro kusan 1,600 suke gudanar aiyukan tsaro a gurin wannan biki tare da goyon bayan dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dana Faransa.

Yarjejeniyar zaman lafiyar ta baya bayan na ta samu nasar fiye da shiga tsakani na baya wadanda Faransa da MDD da AU da kuma ECOWAS suka jagoranta kodayake batun sake tsara rundunar sojin kasar da rajistar masu jefa kuria har yanzu suna zaman ababen dake hana ruwa gudu ga aiwatar da yarjejeniyar.

A birnin na Bouake ne kuma a watan yuni aka kai harin roka kan jirgi dake dauke da Soro inda ya tsira da ransa amma wasu masu tsaron lafiyarsa 4 sun rasa rayukansu,duk da haka tsohon shugaban yan tawayen ya nemi kawadda rade radin wanda ya aikata wannan laifi ya kuma yi kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa karkashin shugabancin mDD.

Kasar ta Ivory Coast mai mutum miliyan 16 ta rabe gida biyu net un wani yunkurin juyin mulki da bai samu nasara ba akan shugaba Gbagbo a watan satumba na 2002,wanda kungiyar NF tayi wadda kuma tun a wancan lokaci take rike da arewacin kasar mai arzikin auduga.

A watan Afrilu a matsayin wani matakin farko na sake hadin kan kasar Gbagbo da Soro sun kawadda shinge mai fadin mrabbain kilomita 12,000 daya rabe tsakanin dakarunsu.