1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin Layya A Jamus

January 20, 2005

Ko da yake musulmi kimanin miliyan uku dake Jamus kan shiga doki da murnar bikin babbar salla ta layya, amma yanayin bikin ya banbanta da na sauran kasashen musulmi

https://p.dw.com/p/BvdZ

Musulmi masu tarin yawa ne suka yi cincirindo a gaban wani masallacin Turkawa dake nan birnin Bonn yau da sanyin safiya domin halartar sallar idi. A cikin hudubarsa ta sallar idi limamin masallacin Fehmi Güler yayi wa jama’a dake cikin kayan ado bayani a game da muhimmancin babbar salla ta layya da kuma hudubar ban-kwana da manzon Allah, mai tsira da aminci yayi a aikin hajjinsa na karshe. Limamin dai ya ci gaba ne da cewar:

"Manufar layya ita ce ba wa dukkan mutane damar cin amfanin dabbar da aka yi layya da ita. Manzon Allah, mai tsira da aminci ya ce: idan kun yi yanka sai ku kasa dabbar gida uku. Kashin farko za a raba wa mutanen da ba su da ikon layya saboda dalilai na kudi. Sannan kashi na biyu a raba wa 'yan uwa da abokan arziki. Shi kuwa kashi na uku sai a ajiye wa yara. Wajibi ne kowa-da-kowa ya rabanta daga dabbar da aka yi layya da ita. Kuma da yake ita Jamus kasace ta kiristoci, an yarje wa musulmi su ba wa makobtansu da ba musulmi ba rabonsu na naman layyar."

Bayan hudubar, ba da wata-wata ba, aka i da sallar idi, saboda ma'aikata su samu kafar komawa bakin ayyukansu. A sakamakon haka ba a fuskanci wani yanayi na doki da murna ba. Musulmi ‚yan kalilan ne kan samu hutu daga guraben ayyukansu. Shi dai masallacin na birnin Bonn yana daya ne daga cikin masallatai sama da 800 na gamayyar musulmin Tukiyya dake nan Jamus (DITIB) a takaice. A saboda haka akasarin masu halartar masallacin Turkawa ne. A irin wannan rana da yawa daga cikinsu su kan yi kewar gida, inda bikin ke daukar wani kyakkyawan fasali na doki da murna. Wani Baturke dan tireda da aka yi hira da shi cewa yayi, kimanin kashi 80% na abokan huldar cinikinsa Jamusawa ne kuma a saboda haka ba zai iya daukar hutu ba. Sai ya kara da cewar:

Ba shakka abin na da radadi. Da so samu ne da zai kaunaci halartar sallar idi, sannan in ziyarci sauran ‚yan uwana. Amma hakan lamari ne mai wuya a nan Jamus. Bayan na sauka daga bakin aikina a wajejen karfe goma na dare zan ziyarci baba ta sannan in zarce zuwa gida.

Amma fa duk da haka akwai wasu musulmin, wadanda duk da matsalolin dake akwai suke dokin bikin sallar sosai da sosai, inda su kan shirya liyafa su kuma gayyaci ‚yan uwa da abokan arziki bayan sun sauko daga bakin ayyukansu.