1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin marubuta adabi a Berlin

Awal (Hon.)October 16, 2008

A bana bikin ya mayar da hankali ne kan nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/FbBV
Bikin buɗe baje kolin marubuta adabi a BerlinHoto: Leo Seidel

A farkon wannan wata na Oktoba a Berlin babban birnin tarayyar Jamus aka gudanar da bukin marubuta adabi karo na duniya. Bukin na bana wanda aka ɗauki kwanaki 10 ana yi shi ne irinsa na takwas a fadar gwamnatin ta Jamus. A wannan karon an maida hankali ne kann nahiyar Afirka da kuma irin gudunmawar da marubuta adabi na wannan nahiya suka bayar ga wannan fanni.

Kamar yadda wataƙila kuka a ji a shimfiɗar shirin a yau za mu leƙa zauren al´adu ne na birnin Berlin inda a farkon wannan wata aka kwashe kwanaki 10 ana gudanar da buki karo na takwas na marubuta adabi na duniya. A bana dai an maida hankali ne kan nahiyar Afirka. An daɗe ana ƙorafin cewa ba a ba da muhimmanci ga rubuce rubucen ´yan Afirka a wannan ƙasa. Wasu na zargin cewa masu karanta littattafai na watsi da karanta duk wani abu daga nahiyar sannan ga Turawa kuma nahiyar ta Afirka na matsayin wani yanki ne in ban da tashe tashen hankula da bala´o´i daga indallahi babu wata gudunmawa da take bayar a gamaiyar ƙasa da ƙasa.

Masu shirya wannan bukin sun bi diddigin waɗannan ƙorafe-ƙorafen, inda suka gano cewa babu gaskiya a ciki, domin a cikin shekaru 20 da suka wuce ´yan Afirka huɗu suka samu kyautar Nobel da ake bawa marubuta adabi. Cikinsu akwai Wole Soyinka da Najib Machfus da Nadine Girdime da kuma John M. Coetzee. To sai dai duk da haka marubuta da mawallafa na nahiyar ta Afirka na fama da matsaloli wajen fassara rubuce-rubucensu a wajen nahiyar don samun masu karantawa.

Bisa al´ada dai adabin harsunan Afirka da aka rawaitosu a baka na matsayin tatsuniyoyi haɗe da kiɗe-kiɗe da waƙoƙi da rawar gargajiya. Rubutaccen adabin kuwa an fi samunsu ne cikin harsunan turawan mulkin mallaka. Wasunsu sun yi ta ba da tarihin lokacin mulkin mallaka da yaƙe-yaƙe da kuma halin da ake ciki bayan samun ´yancin kai. Wasu batutuwan kamar gurɓacewar al´adun gargajiya da tsarin zamantakewar iyali da rayuwa a cikin manyan birane sun taka muhimmiyar rawa a rubutacen adabi na wannan nahiya.

A bukin na bana baya ga wakilan fitattu kuma tsofaffin marubuta adabi kamar Chinua Achebe da Ama Ata Edoo da Nuruddeen Farah da Femi Osofisan da Wole Soyinka, wasu marubuta sababbin jini daga nahiyar ta Afirka sun baje kolin ayyukansu. Daga cikinsu akwai Fatou Diome daga ƙasar Senegal, wadda ta shahara a duniya sakamakon littafinta mai taken “Tumbin Teku.”

Fatou Diome a gun bukin na birnin Berlin ta yi magana game da littafinta na biyu mai taken Ketala. A jawabin da ta yi Fatou ta yi magana game da ƙaura daga Afirka zuwa Turai da wasu ke mata kallon wata Aljanar duniya. Ta kuma yi tsokaci game da rawar da har yanzu cinikin bayi ke takawa a hulɗar dangantaku tsakanin Turai da Afirka.

“Gaskiya ne a matsayina na ´yar Africa , na san da mun girma cikin tarihin baƙar fata kuma za mu mutu a kan labarin tarihin, ni na yi karatu sosai a kan labarin baƙar fata na san da batun bauta saboda abu ne da aka yi, na san da batun bautar da baƙar fata da aka yi ba abu ba ne mai kyau, na san har yanzu mulkin mallaka da turawa suka ma baƙar fata saboda na san irin cin zarafin da aka yi musu a wannan fanin. Idan muka san haka, mi za mu yi? Za mu tsaya kullum muna tunani da abubuwan baya? Ko muce sai mun rama? Ina tsaammanin abin da ya kamata shi ne, mu san cewa da akwai wannan tarihi, saboda mu san mai ya kamata mu yi? Don ka da mu faɗa tarkon jiya, ba za mu tsaya ba, muna tunanin baya don ba kyau. Ya kamata a matsayina na ´yar Afrika, in buga gaba in nuna jin daɗin matsayina, in daraja kaina gaban sauran jama,a saboda ina da ´yanci, wannan ´yancin abu ne da zan nuna a game da zamantakewata, amma ba za ka ce kana da ´yanci kuma zamantakewar ka sai an nuna maka. Ni na san tarihina daga farko har yanzu ba za ni matse kaina ba a cikin wannan rayuwar.”

Helon Habila ɗan Nijeriya wanda yanzu haka yake koyar da adabi a jami´ar George Mason dake birnin Washington ya yi bambamta yanayin aikinsa ne a ƙasarsa ta asali da kuma wajenta. Habila wanda a rubuce rubucensa ya fi mayar da hankali kan batutuwan siyasa ya ce littafinsa na farko a gida ya rubuta amma ba a buga shi ba sai bayan da yayi ƙaura.

"Na rubuta littafin a game da mulkin soji a Nijeriya domin a lokacin soji ne ke mulki a ƙasar. Abokai na waɗanda aka taɓa ɗauresu a kurkuku sun taimaka min da wasu labarai sannan ni kai na na shaida abubuwan da suka faru, shi ya sa na samu sauƙin rubuta littafin. Amma a littafi na biyu da yake a wajen Nijeriya na ke a dole na dogara ga labarai da na samu daga hirarraki ta wayar tarho da kuma tunani na."

Ita kuwa Henriette Rose-Innes daga ATK wadda a bana ta samu kyautar marubutan littattafai na Cain ta yi nuni da cewa ita kam ba ta bari batun siyasa ko tabon mulkin wariyar jinsi a ATK ya shafi aikinta.

“Ba na jin dai zan iya ´yantad da kai na daga wannan abu. Kowane labari yana da wani matsayi a siyasance shi yasa ba abin da zan iya ƙaurace masa ba ne. To amma a rubuce rubuce na ba na ba da muhimmanci ga siyasar Afirka ta Kudu. Ga tsofaffin marubutanmu waɗanda suka yi rayuwa lokacin mulkin wariya ya zama musu dole su taɓo wannan batu. To amma tun bayan shekarar 1994 an samu ɓullar sabbin marubuta waɗanda ke bawa batun siyasar sabon fasali. To sai dai ni nafi sha´awar rubuta gajerun labarai maimakon duba batutuwa na siyasa.”

Banda littatafan da aka baje su an kuma tabka muhawwara a wajen bukin inda Kossi Efoui daga Togo amma yanzu haka yake Faransa ya yi magana game da ´yan Afirka marubuta na cikin gida da na waje inda ya ce tun yana ƙarami yake sha´awar karance karance.

"Tun ina ƙarami na fara bincike akan littattafai na boko. Allah kaɗai ya san yadda na ke jin daɗin wannan binciken. Da yawa dai yara idan sun ga littafi sai su zata abin wasa ne. Abin da ya burgeni na fara rubutu da karatu shi ne ina so in rubuta abubuwa masu ƙayatar da jama´a da jan hankali."