1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar Bastille ya kankama a Faransa

Yusuf Bala Nayaya
July 14, 2017

Faretin da za a yi a Champs-Elysees da zai tuni da cikar shekaru 100 bayan da Amirka ta shiga yakin duniya na daya zai nuna kwalliya ta dakaru a kan dawaki da nuna gwanewa a sarrafa jiragen soja.

https://p.dw.com/p/2gWBI
Frankreich Paris Nationalfeiertag Emmanuel Macron
Hoto: Reuters/S. Mahe

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya halarci bikin ranar Bastille tare da takwaransa na Amirka Donald Trump inda suka kalli fareti soja kafin daga bisani bikin tunawa da shekara guda da kai hari a birnin Nice.

Faretin da za a yi a Champs-Elysees da zai tuni da cikar shekaru 100 bayan da Amirka ta shiga yakin duniya na daya zai nuna ado ko kwalliya ta dakaru a kan dawaki da ma nuna gwanewa a sarrafa jiragen soja.

Shugaba Macron zai yi jawabi a wajen wannan taro da ke zuwa a ranar hutu a kasar da kuma ta zo daidai da bikin tunawa da harin birnin Nice, don haka ma akwai jami'an tsaro 130,000 da aka jibge kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan Faransa ta nunar.