1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar haihuwar rundunar sojan Jamus

November 11, 2005

Bikin cika shekaru hamsin da kafa rundunar sojan Jamus

https://p.dw.com/p/Bu4I
Sojan Jamus
Sojan JamusHoto: AP

Shekaru hamsin bayan kirkiro rundunar sojan Jamus, wato Bundeswehr, har yanzu dai babu wata dangantaka ta kusa, tsakanin rundunar da sauran al’ummar wannan kasa. Sakatare-Janar na kugiyar NATO, Jaap de Hoop Scheffer, dake jawabi a wurin bikin cikar ta shekaru hamsin, ya kwatanta rundunar ta sojan Jamus a matsayin runduna ce ta zaman lafiya, wadda ta samarwa kanta mutunci da daraja a Jamus da kungiyar NATO da kuma duniya baki daya.

Werkhäuser tace sai dai kuma duk da wannan daraja da mutunci da sakatare janar na kungiyar Nato yace rundunar ta sojan Jamus ta samarwa kanta tun da aka kirkiro ta a shekara ta 1955, amma a tsakanin al’ummar Jamusawa rundunar dai bata daukar hankali: Jamusawa da yawa basa nuna wata sha’awa kanta, sa’annan wasu kyamar ta ma suke yi. Ana dai iya cewar masu nuna rashin kaunar su ga rundunar ta Bundeswehr suna hakan ne tare da sanin tarihin Jamus na zamanin mulkin yan Nazi, wanda al’amari ne da ya jefa masu kishin kasar ta Jamus ya zuwa ga daukar matakai na rashin imani da aikata manyan laifuka.

Lokacin da rundunar ta sojan Jamus a karshen watan Oktober tayi bikin cikar ta shekaru hamsin, tare da gagarumin farati, a gaban majalisar dokokin Jamus, wato Reichstag a Berlin sai da aka toshe duk hanyoyin dake isa majalisar dokokin, domin kare wnanan biki daga marasa kaunar faratin, ko kuma ganin an gudanar dashi. A kewayen majalisar dokokin, duk inda mutum ya duba, babu abin da ake gani sai sojoji da tituna da aka toshe su, domin hana wani ya kusanci dandalin faratin, in banda manyan baki da aka gaiyata.

To amma abin tambaya shine, shin wane abokin gaba rundunar sojan Jamus take dashi, har yadda ba zata iya gudanar da bukukuwan ranar haihuwar ta lami lafiya cikin lumana, gaban majalisar dokoki ba. Tsawon shekaru hamsin, rundunar ta sojan Jamus, ta kasance runduna ce dake karkashin umurnin majalisar dokoki. Majalisar ce take kula da aiyukan ta, kuma take, sanya ido a kanta. Wannan kuwa hali ne da ya samu, sakamakon darasin da Jamus ta koya daga tarihin ta. To amma al’ummar kasa sun kasa lura da haka,, kamar dai yadda yakka aka gani, sakamakon zanga-zanga mai tsanani a lokacin babban faratin na gaban majalisar dokoki a Berlin. Da zaran an fara kada badujala, ko sojojin sun fara bushe-bushe, wasu Jamusawa marasa tunani, sukan shiga zanga-zangar nuna adawa da abin da suke ganin kamar dai kokarin Jamus ne na maida kanta kasa mai gwada karfin soja. Hatta wasu yan majalisar dokokin daga jam’iyar nan ta masu ra’ayin canji, sun nuna adawar su da farastin ranar haihuwar rundunar ta Bundeswehr, maimakon su fahimci cewar tsarin da aka yi na mika rundunar karkashin kulawar majalisar dokoki al’amari ne da ya dface, ya kuma zama mai matukar amfani a tsawon shekaru hamsin da tayi tun da aka kafa ta.

Ko da shike ana iya zargin rundunar ta sojan Jamus da wasu laifukan dabam, amma babu shakka cikin irinh wadannan laifuka, babu wadanda suke nunar da cewar rundunar bata son canji, ko kuma tana neman wuce gona-da-iri a kokarin nemarwa kanta suna. A lokacin wannan biki, sojojin basu yi dogon farati kann titin Unter den Linden ba, jiragen saman yaki basu yi ta shawagi a sararin samaniya ba, kamar yadda aka saba gani a wasu kasashe. A maimakon haka, rundunar tayi shekara guda ne tana bikin ta ba tareda ta dauki hankalin kowa ba, kamar dai yanna take a tsawon shekaru hamsin na rayuwar ta.

Jamusawa da yawa suna kyama ko nuna rashin kaunar su ga rundunar ta tsaron Jamus ne ko kuma duk wani abin da ya shafi aikin soja, musamman bikin da aka yi a gaban majalisar dokoki ta Reichsstag, bisa lura da tarihin Jamus a zamanin mulkin yan Nazi. To amma a yau, shekaru sittin bayan kare yakin duniya na biyu, kuma shekaru hamsin bayan kirkiro rundunar ta sojan Jamus, ya zama wajibi ne a janye gaiyatar da aka yiwa al’ummar kasa zuwa ga wnanan biki da kuma nuna amincewar su ga aiyukan da rundunar tayi tsawon shekaru hamsin.

Ko da shike wadanda suka fito fili suka nuna adawar su ga runduar ta sojan Jamus yan kalilan ne, to amma a daya hannun, masu kyamar wannan runduna suna da yawan gaske, har yadda yake shugaban kasa, a lokacin jawabin sa wurin bikin ya zama tilas yayi magana game da haka. Yace da alama Jamusawa basu damu ba, da irin aiyuka masu nagarta da rundunar ta sojan Jamus take yi na kiyaye zaman lafiya a kasashen ketare.

Ko da shike a tsakanin shekaru hamsin da suka wuce zuwa yanzu, Jamusawa miliyan tara ne suka bada gudumuwa a rundunar ta sojan Jamus, amma har yanzu al’ummar kasa basu fahimci gagarumin nauyin dake kann duk wani soja a kasar ba: misali, inda suke sadaukar da rayukan su domin rage matsalar yake yake a wasu yankunan dabam, wanda mataki dake taimakawa ga kara tabbatar da tsaro ga ita kanta Jamus.