1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar mata a duniya

Ramatu Garba Baba
March 8, 2018

Ranar 8 ga watan Maris na kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin biki da nazari na ci gaba ko akasin haka da nufin tabbatar da cewa mata na samun hakkokinsu.

https://p.dw.com/p/2txAe
DR Kongo Vergewaltigungsopfer
Hoto: Imago/ZUMA Press

A irin wannan rana ana bitar nasarori ko kuma kalubale da aka samu a kokarin inganta harkokin mata da fito da matakai na magance cin zarafin mata wanda ke zama ruwan dare gama duniya musamman a wasu kasashen nahiyar Afirka kamar Najeriya da Nijar.

Bikin na wannan shekara na zuwa ne a daidai lokacin da ake alhinin sace wasu ‘yan mata dalibai 110 a makarantar sakandaren Dapchi na jahar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, inda har ya zuwa wannan lokaci babu sahihin labari na inda suke ko halin da suke ciki.

Nigeria Chibok-Mädchen in Abuja
Wasu daga cikin 'yan sakandaren Chibok da aka cetoHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Aghaeze/

Lamarin sace 'yan makarantar Dapchi na zuwa ne kusan shekaru hudu da aka sace dalibai ‘yan mata a makarantar sakandaren da ke Chibok a jihar ta Borno, duk da cewa an yi nasarar 'yanto wasu daga cikin 'yan matan 210 akwai sauran ‘yan mata sama da 100 a hannun kungiyar Boko Haram.

Bugu da kari, an gano yadda ake ci gaba da amfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake ko kuma karuwar matsaloli na fyade musamman a sansanonin ‘yan gudun hijira a Najeriya. Ana kuma alakanta yawancin matsalolin da ake samu na mata da rashin samun ilimi da kuma talauci da kuma al'adar yin shiru in abu ya faru, abin da ake ganin yana taimakawa karuwar ayyukan cin zarafin mata.

Frauen demonstrieren in Khartum, Sudan
Boren adawa da daurin wata 'yar jarida da ta sanya wando a SudanHoto: AP

A sakonsa na bikin wannan rana, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce "kokarin cimma nasarar samar da daidaito da kuma karfafa gwiwar mata da ‘yan mata bai taka kara ya karya ba a lokacinmu, kuma haka shi ne babban kalubale na keta hakkin bani Adama da muke fuskanta.”