1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin rarraba rukunnan wasan kwallon kafa na duniya a Jamus

December 10, 2005
https://p.dw.com/p/BvHC

An yi bikin rarraba kasashe 32 da zasu kara a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za´a yi a badi a nan Jamus idan Allah Ya kaimu. Jamus mai karbar bakoncin wasannin zata bude gasar cin kofin kwallon kafar na shekara ta 2006, inda zata kara da kasar Costa Rica a birnin Munich a ranar 9 ga watan yuni, wato watanni 6 daidai bayan bikin rarraba yadda wasannin farko zasu kasance, wanda aka yi jiya da daddare a birnin Leipzig. Brazil mai rike da kofin duniya a yanzu zata yi wasan ta na farko ne da Kuratiya a ranar 13 ga watan yuni a birnin Berlin. Masana kwallon kafa sun bayyana rukuni na uku wato group C wanda ya hada kasashen Argentina, NL, Serbia-Montenegro da kuma Ivory Coast da cewa ya fi ko-wane daga cikin rukunnan 8 zafi. Daga cikin kasashen da zasu wakilci Afirka a gasar cin kofin kwallon kafar akwai Ghana, Togo, Angola, Ivory Coast, wadanda dukkan su zasu shiga gasar a karon farko sai kuma kasar Tunisia.