1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin shekaru 50 da samun mulkin kan ƙasar Gahana

March 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuQW

Jamaá a ko ina a faɗin ƙasar Ghana na gudanar da shagulgulan cikar ƙasar shekaru 50 da samun mulkin kai daga Britaniya. Ghana ita ce kasa ta farko a nahiyar Afrika wadda ta fara samun mulkin kai daga turawan mulkin mallaka, wanda ya share fage ga sauran ƙasashe da suka biyo baya ta neman yanci. Shugabanin ƙasashe fiye da 20 ke halartar bikin tare da sauran manyan shugabani da shahararrun mawaka da suka hada da Stevie Wonder da kuma shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya Pele. Tuni wasu daga cikin shugabanin Afrika da suka haɗa da shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe da Olusegun Obasanjo na Nigeria da kuma shugaban ƙasar Gabon Omar Bango suka isa ƙasar ta Ghana. Sai dai kuma wasu yan ƙasar ta Ghana na ƙalubalantar makudan kuɗaɗen da aka kashe kimanin euro miliyan 15 a hidimar bikin wanda suka ce kamata yayi a yi amfani da su wajen samar da ruwan sha da wutar lantarki ga jamaá. Ghana ta dade tana fama da matsalar wutar lantarki a fadin ƙasar.