1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin tunawa da gina katangar Berlin

August 13, 2010

A ranar 13 ga watan Agustan 1961 ne dai hukumomin tsohuwar ƙasar jamus ta gabas suka gina wannan katanga

https://p.dw.com/p/OnDC
Hoto: AP

An gudanar da bikin cika shekaru 49 da fara gina katangar Berlin. A lokacin wannan biki na yau, magajin garin na Berlin Klaus Wowereit yayi kira ga jama'a da suci gaba da tunawa da tarihin gina wannan katanga, wanda yace zaici gaba da kasancewa matashiya ga tsarin mulkin demokiradiya da kuma yancin al'umma.

A lokacin wannan biki, an ɗora furanni a dai dai gurin da jama'ar Berlin ta gabas ke neman tsallaka katangar ta Berlin domin shiga yanmaci suka rasa rayukan su.

A ranar 13 ga watan Agustan 1961 ne dai hukumomin tsohuwar ƙasar jamus ta gabas suka gina  wannan katanga da ya raba biranen biyu na shekaru 28 kafin rugujewar katangar ta Berlin da kuma haɗewar jamus ta gabas da ta yanma waje ɗaya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed