1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin tunawa da harin Jirgin kasa a Madrid

March 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuPs

A kasar Spain an gudanar da bukin zagayowar shekaru uku da harin jirgin kasa a birnin Madrid wanda ya kashe mutane 191 da jikata wasu mutanen kimanin 2,000. An kaddamar da wani dandali na Glass dauke da sakwanni na taáziya da jamaá suka rubuta yan kwanaki bayan harin. Sarki Juan Carlos da Sarauniya Sofia da manyan jamián gwamnati suka jagoranci bikin wanda ya sami halartar daruruwan jamaá a wajen tashar jirgin kasa na Atocha, daya daga cikin wurare hudu na harin taáddancin. A ranar 11 ga watan Maris shekara ta 2004 wasu jerin bama bamai suka fashe a cikin jirgin kasar fasinja a birnin Madrid wanda ke zama harin taáddanci mafi muni a nahiyar turai. A halin da ake ciki ana tsare da mutane 29 wadanda ake tuhuma da hannu a wannan hari.