1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin tunawa da ta´asar kisan kiyashin ´yan Nazi

January 28, 2006
https://p.dw.com/p/BvAZ

A jiya juma´a a ko-ina cikin duniya aka yi bikin tunawa da wadanda ta´asar ´yan Nazi ta rutsa da su. Shugabanni sun yi amfani da wannan dama wajen sukar lamirin shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad wanda ya karyata aukuwar kisan kare dangi da aka yiwa Yahudawa sannan ya baiyana hakan da cewa almara ce kawai. Yayin wannan buki a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag shugaban majalisar Norbert Lammert ya baiyana kalaman shugaba Ahmedi-Nijad da cewa ba abin karbuwa ne. Ya ce idan shugabannin na baiyana aukuwar kisan kare dangi da cewa almara ce, to ya zama wajibi Jamus ta karfafa ´yancin wanzuwar Isra´ila a doron kasa. Shi kuwa babban sakataren MDD Kofi Annan kira yayi ga dukkan masu musanta kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawan da su sake tunani. A karon farko a bana MDD ta sanya ranar 27 ga watan janeru ta zama ranar duniya ta tunawa da wannan ta´asa. A wannan rana ce a shekarar 1945 sojojin TS suka ´yantad da sansanin gwale-gwale na Auschwitz.