1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin tunawa da yunkurin halaka Adolf Hitler a ran 20 ga watan yulin 1944

Mohammad Nasiru AwalJuly 20, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhw
Shugaban Jamus Horst Köhler ya na dora furanni a gaban allon tunawa da mutanen da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin ´yan Nazi
Shugaban Jamus Horst Köhler ya na dora furanni a gaban allon tunawa da mutanen da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin ´yan NaziHoto: AP

An dai gudanar da wannan bikin ne na yau a daidai wurin da aka aiwatar da hukuncin kisa akan Claus Schenk Graf von Stauffenberg da mukarrabansa su 3 shekaru 60 da suka wuce. A ran 20 ga watan yulin shekara ta 1944 yunkurin da suka yi na halaka Adolf Hitler ya ci-tura, amma har yau ana yabawa irin bijimtar da suka yi inji Klaus Wowereit magajin garin birnin Berlin.

"Ko da yake ba´a yi nasara ba a yunkurin kifar da gwamnatin ´yan Nazi, amma ba abu ne da ya tafi a banza ba. Mutane maza da mata da suka nuna bajimta a ran 20 ga watan yulin shekara ta 1944 sun nuna alamun ´yantarwa da mutunta dan Adam a daidai lokacin da Jamus ta ke karkashin mulkin ´yan kama karya."

Shi kuwa a cikin jawabinsa na tunawa da gwarzaye shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder cewa yayi mutane kalilan ne ke da irin wannan bajimta ta nuna adawa da Hitler, kuma har yanzu ana tune da wannan bajimta ta ran 20 ga watan yulin shekarar 1944.

"Har wayau abubuwan da suka wakana a ran 20 ga watan yulin na nan kamar sabon abu a garemu, wanda ke bamu karfin guiwar kare mulki na mutuntan ´yancin dan Adam da kuma nuna juriya."

Schröder yayi tuni da irin mawuyacin hali da mutanen da suka ta da boren suka shiga sakamakon rashin samun nasarar yunkurin da suka yin na halaka Hitler. Schröder ya ce sadaukar da rayukan su da suka yi ya bayanar da irin rawar da masu adawa da mulkin kama karya na Hitler suka taka a kokarin samar da wata makomar siyasa mai alfanu da kuma jin dadadin jama´a.

"Wannan bajimtar zata ba mu karfin guiwar nuna adawa da ko-wane irin mulki na kama karya da take hakkin dan Adam. Alhakin da ke kanmu musamman dangane da gudummawar da kasashen Turai suka ba mu, shi ne mu yi kokarin tabbatar da hadewar nahiyar Turai baki daya."

Shi kuwa a nasa bangaren shugaban Jamus Horst Köhler ya bayyana ranar 20 ga watan yulin shekarar 1944 a matsayin wata rana mai muhimmanci a tarihin Jamus. A karshe shugaban na Jamus ya ajiye furanni a gaban allon da aka rubuta sunayen mutanen da aka yiwa kisan gilla.