1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin zagayowar ranar al'uma ta duniya

July 11, 2017

Yayin da ake bikin ranar yawan al'uma a duniya a bana, masana a Nijar da Najeriya na nuna damuwa kan yawan haihuwa da kauracewa kananan garuruwa da matasa ke yi da su ke cewa barazana ce ga ci gaban arziki a kasashen.

https://p.dw.com/p/2gMPJ
Niger Demonstration für Bildungsreform
Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar na daga cikin jihohin da ke da yawan jama'a a kasar, kuma alkaluman sun nuna cewa kowace mace a jihar na haihuwa tsakanin 'ya'ya Bakwai zuwa Takwas, abin da ke sa yawan al'uma ke bunkasa ba kakkautawa. Wannan batun a cewar kwararu na tasiri sosai a kan rayuwar al'umma da ke zama wani babban kalubale ga ci gaban kasa mai fama da koma baya a fannoni daban-daban. Jama'a da dama na birni da na karkara sun halarci bikin wannan ranar a Maradi inda suka saurari jawaban wayar da kai a kan amfanin tsara iyali da ke ci gaba da fuskantar turjiya daga wasu kungiyoyin addini. Sai dai Ustaz Djibril Issa Bana mai bai wa Minista  shawarwari a kan addini ya warware zare da abawa a kan wannan zancen.

Venezuela Zika-Virus
Hoto: picture-alliance/AA/C. Becerra

Bayan taron, ministar kula da yawan al'uma a jamhuriyar ta Nijar madam Rakiyatu Kristelle Jaku, ta ziyarci a gidan nakasasu inda can ma ta yi kira a gare su a kan sanya 'ya 'yansu mata makaranta da kuma batun tsarin iyali. Tassiu Mamman Kashi shugaban kungiyar guragu ya ce su kam sun yi na'am da sakon ministar ta al'uma a kan tsarin iyalin. Yanzu haka dai Jamhuriyar Nijar na kunshe da al'uma da ta zarta miliyon goma sha bakwai  kuma a cewar masana masu hasashen a ma'aikatar kididiga, irin yadda al'umar ke bunkasa, Nijar za ta kai yawan mutum milliyon 94 nan da shekaru 50 masu zuwa, nazarin kuma da ke nuna irin jan aiki da ke gaban kasar.