1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike kan tada bam a Dortmund

Salissou Boukari
April 12, 2017

'Yan sanda a nan Jamus na ci gaba da neman mutumen ko mutanin da ke da hannu wajen dana bam da ya tashi daf da motar 'yan kwallon kafa ta Club din Borrusia Dortmund da yammacin ranar Talata.

https://p.dw.com/p/2b5vO
Nach Explosionen an BVB-Bus
'Yan sandan kasar Jamus na bincike kan harin da aka kaiHoto: picture alliance/dpa/R. Vennenbernd

Harin da ya yi sanadiyyar jikkata Marc Bartra, daya daga cikin 'yan wasan mai shekaru 26 da haihuwa jim kadan kafin wata karawa tare da 'yan wasa na AS Monaco a wasan na kusa da na kusa da na karshe na gasar zakarun Turai. A halin yanzu dai binciken ya bada karfi ne kan wata wasika da aka samu a wurin jim kadan bayan afkuwar lamarin.

Mai magana da yawun 'yan sandan birnin Dortmund Cornelia Weigandt ta yi takaitaccen bayani ga manema labarai inda ta ke cewa "Lalle mun ga tashin bama-baman guda uku, kuma mun samu wani abu a wurin sai dai ba''. Wasikar dai da aka samu ta dauki nauyin harin a cewar Sandra Lücke wata mai bincike sai dai ba ta sanar da abun da wasikar ta kunsa ba.