1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BINCIKEN ALMUNDAHANAR MAN FETUR DIN KASAR IRAQI

March 26, 2004
https://p.dw.com/p/Bvl2

A cikin wan nan makon ne ake sa ran sakataren mdd Kofi Anan zai gabatar da cikakken bayani ga mambobin zartarwa na majalisar, dangane da harkalla data gudana na cin hanci da karbar rashawa bisa matakin nan na sayar da man fetur din kasar iraqi a madadin kawo musu abinci izuwa kasar a shekara ta 1996.

A cewar kakakin majalisar Fred Eckhard,sakataren na mdd tuni ya kammmala tunanin yadda za,a kaddamar da kwamiti mai zaman kansa a majalisar da zai bi kadin wan nan almundahanar da aka tafka a yayin gudanar da wan nan tsari karkashin lemar ta mdd.

Kofi Anan dai ya tabbatar da cewa kaddamar da wan nan kwamiti zai taimaka wajen gano gaskiyar abin da yafaru a lokacin wan nan almundahana da kuma wadanda suke da hannu a ciki;tare da sanin matakin daya kamata a dauka.

Wan nan dai mataki da sakataren na mddd ya dauka ya biyo bayan wani labari ne da wata jaridar kasar ta iraqi mai suna Al Mada ta bugane, dangane da wan nan almundahana da aka tafka a yayin gudanar da wan nan tsari kann man fetur din kasar ta iraqi.

Jaridar ta Almada ta bayyana cewa akwai jamiai kusan 270 daka kasashe sama da 46 a duniya dake da hannu a cikin wan nan almundahanar,da suka hada da yan jaridu da wakilan majalisar dokoki da kuma yan siyasa,da akewa wan nan zargi na karbar cin hancin da kuma rashawar.

Daga cikin wadan nan mutanen a cewar jaridar akwai shugaban hukumar gudanar da wan nan tsari,wato Benon sevan.amma a hannu daya tuni jamiain ya karyata wan nan zargi da cewa baya da tushe balle makama.

Wan nan dai tsarin na sayar da man fetur din kasar ta Iraqi a maimakon kawo musu abinci an fara shine a yayin da kasar ta iraqi ke cikin halin kakanikayi na dabaibayin takunkumi da mdd ta kakaba mata wanda ya danganci tattalin arziki.

A yanzu haka dai da dama daga cikin mambobin kwamitin sulhu na mdd sun nuna ammanar su dangane da kafa wan nan kwamiti bisa hujjar tantance gaskiyar wan nan al,amari.

Shi kuwa shugaban kwamitin na wan nan lokaci,wanda kuma jakadane na kasar Faransa wato Jean Marc de la Sablliere,bukatar sakataren na mdd yayi daya duba yiwuwar zuwa da kai wanda hausawa kance yafi aike don yiwa mambobin jawabi dangane da wan nan harkalla dalla dalla don fahintar ta so sai da so sai.

A waje daya kuma,wata twaga ta masu bincike da Amurka ta nada kann binciken almundahanar da tsohon shugaban kasar iraqi Saddam Hussin ya tafka bisa wan nan tsari na sayar da man fetur din kasar a madadin kawo abinci na nan naci gaba da gudanar da bincike don kawo rahoton su.

A dai karkashin wan nan bincike ana zargin Saddam Hussain da samun dalar Amurka kusan biliyan goma da digo daya a matsayin riba ta barauniyar hanya a yayin gudanar da wan nan tsari na rage yawan man fetur din da kasar ta iraqi ke sayarwa a lokacin tana cikin dabaibayi na takunkumin tattalin arziki.