1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken cin zarafin Fursunoni a Afghanistan

November 15, 2007
https://p.dw.com/p/CE6z

Shugaban ƙasar Afghanistan Hamid Karzai ya naɗa wani kwamiti wanda zai binciki zargin azabtar da mutanen da ake tsare da su a gidajen yarin ƙasar. Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta duniya Amnesty International, ta yi ikrarin cewa dakarun sojin NATO dana ISAF sun tozarta mutanen da ake tsare da su bisa mika su ga hukumomin Afghanistan. A wata hira da aka yi da shi, kwamandan rundunar ISAF Janar Egon Ramms ya shaidawa tashar Deutsche Welle cewa akwai alamun gaskiya a wasu daga cikin zargin. A saboda haka ya buƙaci hukumomin ƙasar ta Afghanistan su gudanar da harkokin fursunonin bisa yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta kare haƙƙin bil Adama.