1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bindige yaran uku da wasu ’yan bindiga daɗi suka yi a birnin Gaza, ya janyo fusatar shugabanin Falasɗinawa.

December 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuYK

Ɗimbin yawan jama’a da kuma shugabannin Falasɗinawa ne suke ta bayyana matuƙar ɓacin ransu game da bindige yara ƙanana guda uku, da wasu ’yan bindiga daɗi suka yi yau a birnin Gaza. Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya ce kisan yaran, da wasu ’yan bindiga daɗin da ba a gano asalinsu ba tukuna suka yi, wato wani mummunan ɗanyen aiki ne na rashin imani da tausaya wa bil’Adama. Su dai yara ukun da aka bindige, masu shekaru tsakanin 6 da tara da haihuwa, duk ’ya’yan wani babban jami’in leƙen asirin Falasɗinawan ne mai biyayya ga shugaba Mahmoud Abbas. Dubban jama’a ne suka yi zanga-zanga a lokacin jana’izar yaran. Rahotanni sun ce wasu daga cikinsu ma sun kutsa cikin farfajiyar majalisar Falasɗinawan, inda suka yi ta buɗe wuta a kan ginin. Ɗaya daga cikin fararen hular da ke kusa da gun arangamar, ya rasa ransa a harbe-harben da aka yi, sa’annan wasu yara biyu kuma suka ji rauni, inji rahotannin. Kawo yanzu dai, babu wanda ya yi ikirarin ɗaukar nauyin harbe-harben, a daidai lokacin da ake ta ƙara samun hauhawar tsamari tsakanin ƙungiyar Hamas da ke jagorancin gwamnati da kuma rukunin Fatah ta shugaban Falasɗinawan, Mahmoud Abbas.