1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biritaniya za ta miƙa garin Basra ga sojin Iraƙi

Ibrahim SaniDecember 16, 2007
https://p.dw.com/p/CcEt

Nan gaba kaɗan sojin Biritaniya za su miƙa ragamar tafiyar da harkokin tsaro na garin Basra ga sojin Iraqi. Hakan dai zai kawo ƙarshen kasancewar garin Basra ƙarƙashin ikon Biritaniya. Sojin na Biritaniya dai sun shafe a ƙalla shekaru biyar su na gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a wannan yanki. Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce harkokin tsaro a yankin sun inganta. Matakin a cewar bayanai zai kasance babban ƙalubalene ga Gwamnatin Iraƙi. Bikin miƙa yankin ana sa ran zai samu halartar Faraminista Nuri Al Maliki da kuma wasu Jami´an Biritaniya. Rahotanni sun ce bayan miƙa ragamar yankin, sojin Biritaniya dubu biyu da ɗari biyar za su ci gaba da kasancewa a Basra, ragowar rabin kuma su koma gida Biritaniya.