1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biritaniya zata rage yawan sojin ta a Iraq

February 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuRL

Faraminisatan Biritaniya Mr Tony Blair na ya bayyanawa yan majalisar dokokin kasar shirin sa, na fara janye sojin su daga Iraqi.

Mr Blair, wanda ya fadi hakan, yayin da yake gabatar da jawabi a gaban yan majalisun a yau, yace sun dauki matakin ne bisa dalilin cewa babu wata barazana a Basra, inda sojin nasu suke a kasar ta Iraqi.

Kafafen yada labarai na kasar sun sanar da cewa, da alama Biritaniya zata janye kusan rabin sojin nata ne dake Iraqin.

Akwai dai hasashen cewa soji dubu 7 da dari daya ne zasu dawo gida a karshen shekarar nan.

Daga cikin wannan jumla ana sa ran soji dubu 1 da dari biyar zasu fara isowa gida ne, a watan Afrilun wannan shekara.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa tuni Mr Blair ya shaidawa Mr Bush wannan mataki da yake shirin dauka.

A dai lokacin da Biritaniya ke kokarin rage sojojin nata a Iraqi, a dai dai lokacinne kuma ,Amurka ke shirye shiryen kara aikewa da dakarun soji dubu 21 izuwa kasar.