1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birnin Kudus ta zama babban birnin Isra'ila

Abdul-raheem Hassan
December 7, 2017

Shugabannin kasashen musulmai sun yi Allah wadai da matakin Amirka na maida birnin Kudus ya zama babba birnin kasar Isra'ila, kasashen na ganin matakin cire fadar gwamnatin daga birnin Tel Aviv tamkar neman tsokana.

https://p.dw.com/p/2oxRu
Pakistan - Proteste gegen Jerusalem-Status in Islamabad
Hoto: Getty Images/AFP/F. Naeem

Kasashen Turkiyya da Indunisiya na a cikin manyan kasashe da akafi samun yawan musulmai, sun kuma soki matakin da ce wa Amirkar ta saba tsarin Majalisar Dinkin Duniya na tun shekarun 1980 na na sauya birnin kudus a matsayin fadar mulkin Isra'ila.

Tun bayan bayyana sauya birnin na Kudus a matsayin fadar mulkin Isra'aila, Falasdinawa ke zanga-zangar adawa da kudurin na Amirka.