1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya da Holland sun yi kira ga sauran ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Kan Turai da su taimaka wajen tabbatad da zaman lafiya a Afghanistan.

November 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buc7

Ƙasashen Birtaniya da Holland sun shawarci sauran takwarorinsu na Ƙungiyar Haɗin Kan Turai da su ƙara taimakawa wajen tabbatad da zaman lafiya a Afghanistan. Amma Faransa na ɗari-ɗari ga kiran da ƙungiyar ƙawance ta NATO ta yi na tura wata tawaga daga ƙungiyar EUn ɗin zuwa Afghanistan don ta horad da jami’an tsaro da kuma na shari’ar wannan ƙasa. A halin da ake ciki dai EU ta ce za ta tura jami’anta zuwa birnin Kabul don su yi nazarin kan bukatun da akwai na horad da jami’an da kuma irin angizon da yin hakan zai samu a ƙasar.

Ministan tsaron Jamus, Franz Josef Jung, ya ce yana marhabin da ƙarin taimakon da ƙungiyar EUn za ta bai wa jami’an ’yan sandanta guda 40, waɗanda a halin yanzu ke horad da takwarorinsu a Afghanistan ɗin. Babban sakataren ƙungiyar NATO, Jaap de Hooop Scheffer kuma, kusan kullun ma sai ya yi ta nanata kiransa ga ƙungiyar EUn da ta ƙara ɗaukar nauyin kare fararen hula a ƙasar.