1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya - EU: Sakamako

December 22, 2005

A ran 31 ga watan Disamba ne Birtaniya za ta cika wa'adin shugabancin Kungiyar Hadin Kan Turai, na tsawon wata shida. Ko wane irin sakamako ne aka cim ma a wannan lokacin ?

https://p.dw.com/p/Bu39
Tony Blair
Tony BlairHoto: AP

Babban nasarar da Birtaniya za ta iya kambama kanta da ita, a karshen wa’adinta na jagorancin kungiyar Hadin Kan Turai, ita ce ta ganin cewa ba a sami cikas a kan batun kasafin kudin kungiyar, a karo na biyu ba. Sai dai, yarjejeniyar da aka cim ma, har ila yau ba za ta iya tabbatad da adalci ga duk mambobin kungiyar ba. A nan kuwa, ba Birtaniyan ce kawai za a iya dora wa laifin rashin samad da ingantacciyar yarjejeniya ba.

Tuni dai, majalisar tarayyar Turan, da taron shugabannin gwamnatoci da na kasashen kungiyar sun gaza cim da wata madafa kan batun kundin tsarin mulkin gamayyar. Bayan da al’umman Faransa da na kasasr Holland suka yi watsi da kundin, a zaßen raba gardamar da aka gudanar a wadannan kasashen, babu wani abin da majalisar ta taßuka kuma. Ta sa ido ne tana zaman `yar kallo kawai. A halin yanzu dai, babu wani mataki da aka dauka na yi wa kundin kwaskwarima. Idan ko ba a yi hakan ba, to batun sake wani zaßen raba gardamar ma ba zai taso ba ke nan. A lokacin wa’adin Birtaniya a jagorancin kungiyar dai, za a iya cewa mahukuntan birnin London ba su nuna sha’awar farfado da tattaunawa kan batun kundin tsarin mulkin ba. Shi dai Tony Blair ya nisanta da kansa ne daga shirya wata sabuwar muhawara, saboda fargabar hakan ka iya janyo masa zaizayewar kwarjini a harkokin siyasar cikin gida. Da farko dai, a lokacin da Birtaniya ta karßi ragamar jagorancin kungiyar a cikin watan Yulin da ya gabata, Tony Blair ya yi jawabi kan muhimmancin da akwai na yi wa tsarin dokokin kungiyar garambawul. Amma tun wannan lokacin, bai ce uffan ba kuma a kan wannan batun.

Yanzu dai ana hasashen cewa, ce ce kucen da aka yi a kan kasafin kudin kungiyar zai karfafa rashin jituwar kasashe da dama mambobin kùngiyar. Har ila yau dai babu wani haske kan rangwamin da wasu kasashe ke samu. A lokacin wa’adinta, Birtaniyan ta yi kokarin takalo batun rashin jin dadin jama’a da kuma sakamakon da hakan ya janyo, a lokacin zaßukan raba gardama a Faransa da kasar Holland. Tony Blair dai, a matsayinsa na shugaban kungiyar Hadin Kan Turan mai barin gado, ya shawarci duk mambobin kungiyar da su dau salon hadayyar tattalin arzkin duniya, wanda aka fi sani da suna globalisation a turance, da muhimmanci don kada a bar su a baya. kalubalen da kasashen Turan za su huskanta a wannan ßangaren dai, shi ne daidaita kasuwar fannin ayyukan da ba na ker-kere ba, wanda a lokacin wa’adin Birtaniyan, babu abin da aka taßuka a kansa.

Wata nasarar da Tony Blair ke kambama kansa da ita kuma, ita ce, wato fara shawarwari da kasar Turkiyya da aka yi game da yunkurin shigowarta cikin kungiyar Hadin Kan Turan. Sai dai a nan ma, har ila yau, mafi yawan al’umman Turan ne ke adawa da batun kara fadada kungiyar. Ba sa dai goyon bayan ra’ayin da Blair din ya gabatar na cewa, shigowar Turkiyya cikin kungiyar na muhimmanci kwarai a huskar tsaro. Yanzu kuma da aka yi zurfi a shawarwarin da ake yi, kan shigowar kasashen Croatia da Macedoniya cikin kungiyar, tambayar da ake ta korafi a kanta ita ce, ina iyakar fadada kungiyar Hadin Kan Turan take ?