1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: Sabbin matakan tada komadar tattalin arziki

November 21, 2016

Firaminstar Birtaniya Theresa May ta sanar da sabbin dubarun jawo hankalin kamfanonin ketare.

https://p.dw.com/p/2T0ml
Indien Großbritannien Besuch von Theresa May bei Narendra Modi
Firaministar Birtaniya Theresa MayHoto: picture-alliance/dpa/H. Tyagi

Firaministar Birtaniya Theresa May ta sanar cewa a shekaru masu zuwa gwamnatin kasar za ta kara yawan tallafin da take ba wa fannin ayyukan bincike da raya kasa. Da wannan kasar ta Birtaniya za ta ci gaba da jan hankalin 'yan kasuwa da kamfanoni bayan ta kammala ta kammala ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai. A lokacin da take jawabi a gun taron kungiyar masu masana'antu ta Birtaniya, Firaminista May ta ce a duk shekara gwamnati za ta tallafa da kudi Euro miliyan dubu 2.3 musamman a fannin sabbin fasahohi na kere-kere da kayan kiwon lafiya har zuwa shekara ta 2020.

"Burinmu ba shi ne tallafa wa masana'antun da ba sa tabuka abin kirkiki ba, abinda muka sa gaba shi ne kirkiro da yanayi da za a samu bunkasa. Za mu ci gaba da mara wa masu samun nasara baya tare da karfafa musu guiwa su zuba jari na tsawon lokaci a Birtaniya domin samar da aikin yi da bunkasar tattalin arziki a kowane lungu da sako na kasar nan."

Wasu rahotanni sun nuna cewa kasar za ta rage yawan haraji zuwa matsayi mafi karanci a jerin kasashe masu ci gaban masana'antu don kwadaita wa kamfanonin kasa da kasa zuwa Birtaniya.