1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta ce za a janye duk dakarun ƙetare daga Iraqi a cikin shekaru 4 masu zuwa nan gaba.

May 22, 2006
https://p.dw.com/p/BuxE

Jami’an gwamnatin Birtaniya na kyautata zaton cewa, mai yiwuwa a janye duk dakarun ƙetare daga Iraqi a cikin shekaru 4 masu zuwa nan gaba. Wannan sanarwar dai ta zo ne a daidai lokacin da Firamiyan Birtaniyan Tony Blair, ya isa a birnin Bagadaza, a wata ziyarar ba zato ba tsammani da ya kai a Iraqin, don nuna goyon bayansa ga sabuwar gwamnatin ƙasar.

A cikin wani jawabin haɗin gwiwar da ya yi da Firamiyan Iraqin Nur al-Maliki, ga taron maneman labarai a birnin na Bagadaza, Tony Blair ya yi alkawarin bai wa gwamnatin Iraqin haɗin kai. A ƙarshen makon da ya gabata ne dai, aka kammala kafa gwamnatin haɗin kan ƙasar, bayan an shafe watanni ana ta muhawara kan yadda za a rarraba madafan iko.

A nasa ɓangaren, Firamiya al-Maliki, ya ce abin da gwamnatinsa za ta fi bai wa fiffiko ne shawo kan tahse-tashen hankulla a duk faɗin ƙasar. Ya kuma faɗa wa maneman labarai cewa, dakarun Amirka, za su miƙa wa jami’an tsaron Iraqin, akalar kula da tsaro a jihohi biyu na kasar tun daga watan Yuni.

Rahotannin da muka samu daga Iraqin sun ce, a daidai lokacin da Tony Blair ya isa a unguwar gwamnati a birnin Bagadaza, an ta da bamabamai biyu a wasu yankuna daban kuma na birnin, waɗanda suka janyo mutuwar a ƙalla mutane 9.