1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta zabi ficewa daga Tarayyar Turai

Salissou BoukariJune 24, 2016

Al'ummar kasar Birtaniya ta kada kuri'un ficewa daga Tarayyar Turai, kamar yadda kwarya-kwaryar sakamakon zaben ya nunar a wannan safiya ta Juma'a.

https://p.dw.com/p/1JCFx
London UKIP Vorsitzender Nigel Farage
Shugaban jam'iyyar UKIP Nigel Farage mai goyon bayan fice wa daga Tarayyar TuraiHoto: picture-alliance/empics/S. Rousseau

Kawo yanzu dai sakamakon ya nunar cewa kashi 52 na 'yan kasar sun zabi fice wa daga kungiyar ta Tarayyar Turai kuma adadin kuri'un da aka kidaya sun tabbatar cewa babu wasu alkalumma da za su iya canza hakan. Ta shafinsa na Twitter, ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya sanar cewa, labarin da ke fito musu daga kasar Birtaniya ba labari ba ne mai dadi ga Tarayyar Turai da ma ita kanta Burtaniya.

Sai dai daga nata bangare shugabar jam'iyyar masu ra'ayin kishin kasa ta kasar Faransa Marine Le Pen, ta shafinta na Twitter ta ce wannan nasara, nasara ce ta 'yanci, kuma kamar yadda ta sha fada shekaru da dama, a yanzu dai ta tabbata cewa ko su a Faransa sai an yi wannan zabe na raba gardama na ficewa daga EU. Wannan labari dai ya saka masu zuba hannayen jari a kasuwannin duniya cikin wani hali na rashin sanin tabbas.