1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya za ta cika yarjeniyoyinta da EU

Abdullahi Tanko Bala
October 20, 2017

A shirye muke mu cika dukkan alkawuran da muka cimma da EU gabanin shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar EU a cewar Firaminista Theresa May.

https://p.dw.com/p/2mFbx
Belgien EU-Gipfel Theresa May und Donald Tusk
Hoto: Reuters/G. Vanden Wijngaert

Firaministar Birtaniya Theresa May ta shaidawa takwarorinta shugabannin EU cewa Birtaniya za ta martaba alkawuran da ta daukarwa gabanin ficewar kasar daga kungiyar EU, ta na mai cewa babu wata kasa da za ta yi hasara a dangane da kasafin kudin da ake aiki da shi a yanzu. 

Abin da na fayyacewa takwarorina na EU a game da biyan gudunmawar kudi shine abin da na zayyana tun farko a jawabi na, cewa babu wani abin damuwa a game da shirin kasafin kudi, walau dai za su biya karin kudade ne ko kuma za su sami raguwar kason kudi a sakamakon ficewar Birtaniya. Za mu martaba dukkan alkawuran da muka dauka a lokacin da muke cikin kungiyar EU inji Theresa May.

A waje guda dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce sai an warware batun sauke hakkin da ya rataya a wuyan Birtaniya na biyan dukkan kudaden da suke kanta kafin a fara wata tattaunawa da ta shafi cinikayya da kasar Birtaniyar.